Cristiano Ronaldo zai Angwance, an Fadi Matar da zai Aura a Portugal

Cristiano Ronaldo zai Angwance, an Fadi Matar da zai Aura a Portugal

  • Rahotanni sun ce fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa Cristiano Ronaldo zai auri budurwarsa Georgina Rodriguez a mako mai zuwa a garinsu na Funchal da ke Portugal
  • Ana sa ran za a daura auren a babban cocin Funchal kafin baki su wuce wani katafaren otal mai matukar girma domin liyafar bikin fitaccen dan kwallon
  • Ronaldo da Georgina sun kara janyo hankalin jama'a bayan da suka nuna zobban lu'ulu'unsu masu tsada gabanin bikin da ake sa ran za su yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Funchal, Portugal – Rahotanni sun bayyana cewa fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Portugal, Cristiano Ronaldo, na shirin ɗaura aure da budurwarsa Georgina Rodriguez a mako mai zuwa.

Ana sa ran za a gudanar da bikin ne a babban cocin Funchal da ke tsibirin Madeira, wanda shi ne garin da Ronaldo ya taso tun yana ƙarami.

Kara karanta wannan

Sababbin bayanai sun fito kan zargin tsohon gwamna game da juyin mulkin Tinubu

Cristiano Ronaldo da Georgina Rodriguez
Cristiano Ronaldo da budurwarsa, Georgina Rodriguez Hoto: Fabrizio Romano
Source: Facebook

Daily Mail ta rahoto cewa bayan ɗaurin auren, baki za su wuce katafaren otal ɗin Savoy Palace domin gudanar da liyafar bikin.

Inda za a gudanar da bikin

Rahotanni sun nuna cewa tun farko an yi hasashen za a yi bikin a Quinta da Regaleira da ke Sintra, amma daga baya an yi watsi da wannan bayanin.

Wata majiya ta bayyana cewa an sanar da baƙin otal ɗin Savoy Palace cewa wasu benaye biyu da wuraren mashaya da dama ba za su kasance a bude ba a ranar Juma'a da Asabar saboda bikin.

Funchal dai shi ne garin haihuwar Ronaldo, inda aka gina masa mutum-mutumi na tagulla tare da sanya sunansa ga wani otal saboda irin gudummawar da ya bayar ga ƙwallon ƙafa.

Ronaldo ya jawo hankalin jama'a

Rahotanni sun ce Ronaldo, wanda dukiyarsa ta kai tsakanin dala biliyan 1.2 zuwa 1.4, ya zaɓi yin bikin a garinsu ne saboda muhimmancin wurin a rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Gwamnatin Tinubu za ta zare tallafin lantarki a 2027

An bayyana cewa ya taso cikin talauci a Funchal, inda ya rika kwana a ɗaki ɗaya tare da 'yan uwansa kafin ya bar gida yana ɗan shekara 11 domin komawa Sporting Lisbon.

Cristiano Ronaldo a filin kwallo
Cristiano Ronaldo yana taka leda a filin kwallo. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A kwanakin baya, Ronaldo da Georgina sun wallafa hotuna daga hutun da suke yi a bakin teku a Portugal, inda suka nuna manyan zobban lu'ulu'unsu, lamarin da ya ƙara ƙarfafa jita-jitar cewa bikin aurensu na gab da gudana.

Dan jarida mai kawo labaran kwallon kafa, Fabrizio Romano ya tabbatar da labarin auren a sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Ronaldo ya kafa tarihi a kwallo

A wani labarin, mun ruwaito cewa Cristiano Ronaldo ya fara buga gasar cin Kofin Duniya ta FIFA a shekarar 2006 da aka gudanar a Jamus.

A shekarar 2026 ya kafa tarihi a matsayin ɗan wasa na farko da ya zura ƙwallo a gasar cin Kofin Duniya har sau shida a jere.

Sai dai duk da dimbin nasarorin da ya samu a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa, Ronaldo bai taɓa lashe Kofin Duniya ba, inda Portugal ta fice daga gasar 2026 ba tare da ta lashe kofin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng