Karfin Hali: Yan Najeriya Sun Dauki Makamai domin Kare Kansu a Afirka Ta Kudu
- Wasu 'yan Najeriya sun shirya kare kansu a kasar Afirka ta Kudu bayan wa'adin 30 ga Yunin shekarar 2026 da aka ba baki
- Kungiyoyin masu adawa da baƙi sun nemi a kori baki ɗaya baƙin da ke ƙasar, yayin da aka kashe wasu 'yan ƙasashen Afirka a hare-haren
- Gwamnatin Najeriya ta sake yin Allah wadai da hare-haren, tare da buƙatar hukumomin Afirka ta Kudu su tabbatar da tsaron 'yan kasarta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Johannesburg, South Africa - Wasu 'yan Najeriya da ke zaune a Afirka ta Kudu sun ƙi barin ƙasar bayan wa'adin 30 ga Yuni.
Rahotanni sun ce sun ce yan Najeriya da dama sun ɗauki makamai domin kare kansu yayin da ake rikicin kin jinin baki.

Source: Twitter
Ana ci gaba da sukar yan Afirka ta Kudu
Kungiyoyin da ke yaƙi da baƙi sun daɗe suna matsa lamba kan gwamnati ta kori baƙi daga ƙasar matakin da ya jawo suka daga sassa daban-daban, cewar Daily Trust.
Ɗaya daga cikin fitattun ƙungiyoyin, March and March, ta yi zargin cewa baƙi marasa takardu suna ƙwace ayyukan yi da sauran damar da 'yan ƙasar suka kamata su samu.
Shugabar ƙungiyar, Jacinta Ngobese-Zuma, ta shaida wa wani taro a Durban cewa suna son a kori baƙi baki ɗaya daga Afirka ta Kudu.
Bayan cikar wa'adin, wasu daga cikin masu zanga-zangar sun kutsa gidaje da otal-otal inda suka yi zargin baƙi sun buya.
Wani bidiyo da ya bazu ya nuna yadda aka kori wani mutum tare da iyalansa, ciki har da ƙananan yara, daga gidansu.
Hukumomi sun bayyana cewa sama da mutum 25,000 sun kammala shirye-shiryen barin Afirka ta Kudu cikin makwannin da suka gabata.

Source: UGC
Matsayar wasu ƴan Najeriya a Afirka ta Kudu
Sai dai wasu 'yan Najeriya sun bayyana cewa ba za su bar ƙasar ba, kuma sun shirya kare kansu idan an kai musu hari.
Wani bidiyo da aka gani ranar Asabar ya nuna 'yan Najeriya da wasu 'yan Afirka ta Kudu suna fuskantar juna, yayin da 'yan sanda suka tsaya tsakaninsu.
Mai sharhi a bidiyon ya ce 'yan Najeriya na jiran ɗaya ɓangaren ya tsallaka layin da aka ware kafin su mayar da martani.
Bidiyon ya kuma nuna wasu daga cikin 'yan Najeriya suna riƙe da adduna da sauran ƙananan makamai domin kare kansu.
An kuma ji ƙarar harbin bindiga a cikin bidiyon, abin da ya ƙara tayar da hankalin mutanen da ke wurin, cewar Daily Post.
Gwamnatin Najeriya ta sha yin Allah wadai da hare-haren da ake kai wa 'yan ƙasarta a Afirka ta Kudu tare da neman a kare rayuwarsu.
Ta hannun Babban Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Pretoria, gwamnati ta shawarci 'yan Najeriya su guji wuraren rikici kuma su kai rahoton duk wata barazana.
Ana ci gaba da farautar yan Najeriya
An ji cewa mutane na gudanar da zanga-zanga a birane daban-daban na Afirka ta Kudu a kan neman baƙin haure su fice daga kasar a gaggawa.
A yanzu haka dubban baƙin haure sun fice daga yankunansu, yayin da wasu mutane suka mutu a zanga-zangar da ake yi a kasar.
Wasu ƙasashen Afirka ciki har da Najeriya sun tura jirage da motoci domin dauko 'yan ƙasarsu saboda tsoron kar a kai masu hari.
Asali: Legit.ng

