Tura Ta Kai Bango: 'Yan Bindiga Sun Tsokano Malamin Addini, Ya Yi Masu Babban Tanadi

Tura Ta Kai Bango: 'Yan Bindiga Sun Tsokano Malamin Addini, Ya Yi Masu Babban Tanadi

  • Bishop David Oyedepo ya ce gwamnatin tarayya ba ta yi abin da ya dace wajen dakile yawaitar kashe-kashe a Najeriya ba
  • Malamin addinin ya ce ba zai yi wa masu kai hare-hare addu'a ba, sai dai zai yi addu'a a kansu da masu daukar nauyinsu
  • Gwamnatin tarayya ta sha yin Allah-wadai da hare-haren ‘yan ta’adda da sauran kungiyoyin masu tayar da hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Bishop David Oyedepo, wanda ya kafa kuma shugaban Living Faith Church Worldwide, ya ce gwamnatin tarayya ba ta yi abin da ya dace ba wajen kawo karshen yawaitar kashe-kashe a fadin Najeriya.

Bishop Oyedepo ya ce wadanda ke da hannu wajen kashe-kashen ba za su yi tsammanin zai yi musu addu'a ba.

Oyedepo ya yi addua kan 'yan bindiga
Babban malamin addinin kirista, Bishop David Oyedepo Hoto: Bishop David Olaniyi Oyedepo
Source: Facebook

Jaridar TheCable ta ce Bishop Oyedepo ya bayyana hakan ne yayin da yake magana yayin ibadar ranar Lahadi ta cocin a ranar 2 ga Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano inda aka boye gawar shugaban al'umma da aka hallaka a Imo

Oyedepo ya ce zai yi addu'a a kan masu kai hare-haren da kuma wadanda ke daukar nauyinsu, jaridar The Punch ta kawo labarin.

Oyedepo ya yi addu'a kan masu kisa

Malamin ya ce:

“Ba za ku kashe ‘yan uwana sannan ku yi tsammanin zan yi muku addu'a ba. Zan yi addu'a a kanku, a kan gidajensu da kuma ahalinku, cikin sunan Yesu.”

Oyedepo ya kuma yi zargin cewa akwai masu daukar nauyin wadanda ke kai hare-haren. Ya ce wadanda ke daukar nauyin masu kai hare-haren za su fuskanci hukuncin Allah.

Oyedepo ya ce lokacin shiru ya wuce

Bishop Oyedepo ya ce ya dade yana yin shiru, amma yanzu lokaci ya yi da Allah zai shiga lamarin.

Ya kara da cewa duk wanda yake aikata mugunta ko daukar nauyin kashe-kashe ba zai sami wurin buya daga fushin Allah ba.

“Kowa ya san cewa ana daukar nauyin wadannan mugayen mutane. Duk wanda bai san hakan ba, to akwai matsala."

Kara karanta wannan

ADC ta bukaci Tinubu ya ceto daliban Borno kamar na Oyo

“Duk wanda ke daukar nauyin masu kisa a Najeriya, la'ana ta sauka a kansa daga yau. Na dade ina yin shiru, amma lokaci ya kusa da komai zai bayyana.”

- Bishop David Oyedepo

Oyedepo ya soki gwamnatin Tinubu

Oyedepo ya soki yadda gwamnati ke mayar da martani kan tabarbarewar tsaro a Najeriya. Ya ce bai ji wata sanarwa daga bangaren gwamnati da ke yin Allah-wadai da kashe-kashen ba.

“Ban ji wata sanarwa daga bangaren gwamnati da ke yin Allah-wadai da kashe-kashen ba. Har yanzu ban ji ko guda ba."
“Shin rayukan mutane ba su da wata kima kuma? Gwamnati tana nuna kamar ba ta san abin da za ta yi ba.”

- Bishop David Oyedepo

Oyedepo ya ragargaji 'yan bindiga
Bishop David Oyedepo na jawabi a wajen taron coci Hoto: Bishop David Olaniyi Oyedepo
Source: Facebook

Sai dai sabanin ikirarin Oyedepo, gwamnatin tarayya ta sha yin Allah-wadai da hare-haren ‘yan ta’adda da sauran kungiyoyin masu tayar da hankali.

Duk da haka, ana yawan sukar gwamnati kan rashin daukar matakan da suka yi daidai da irin kalaman Allah-wadai da take yi.

'Yan bindiga sun sace basarake

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da wani dagaci a jihar Neja.

'Yan bindigan sun sace dagacin ne na ƙauyen Patiko, Mallam Haruna Abubakar, a gundumar Zugurma da ke karamar hukumar Mashegu a jihar Neja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng