Fitaccen 'Dan Kwallo Ya Mutu Kwanaki Kadan bayan Cire Kasarsa a Gasar Kofin Duniya na 2026

Fitaccen 'Dan Kwallo Ya Mutu Kwanaki Kadan bayan Cire Kasarsa a Gasar Kofin Duniya na 2026

  • 'Dan wasan tsakiya na kasar Afrika ta Kudu, Jayden Adams, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 25 da haaihuwa a duniya
  • Ministan Wasanni na kasar Afirka ta Kudu, Gayton McKenzie ya bayyana mutuwar fitaccen ɗan wasan a matsayin babban rashi ga kwallon kafa
  • ‘Yan sanda sun fara bincike bayan an gano gawarsa a wani gida a Cape Town kwanaki kadan bayan an cire kasarsa daga gasar kofin duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

South Africa - Dan wasan tsakiya na kasar Afrika ta Kudu, Jayden Adams, wanda ya wakilci kasarsa a gasar cin Kofin Duniya da ake ci gaba da yi, ya rasu a ranar Asabar yana da shekara 25.

Ministan Wasanni na Afrika ta Kudu, Gayton McKenzie, ne ya tabbatar da rasuwar fitaccen dan wasan cikin wata sanarwa da ya fitar yau Asabar, 11 ga watan Yuli, 2026.

Kara karanta wannan

Yaƙin Amurka da ƙasar musulunci ta Iran ya zama 'alheri' ga attajirin Najeriya, Dangote

Jayden Adams.
Dan wasan tsakiya na kasar Afirka ta Kudu, Jayden Adams a cikin filin kwallo a gasar cin kofin duniya na 2026 Hoto: Jayden Adams
Source: Getty Images

Dan wasan kasar Afirka ta Kudu ya rasu

A rahoton da jaridar Vanguard ta wallafa, ministan ya bayyana rasuwar Adams a matsayin sbin kaduwa kuma babban rashi ga tawagar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu.

Gayton McKenzie ya ce:

"Na samu labarin rasuwar Jayden Adams cikin matukar kaduwa da jimami. Kwallon kafar Afrika ta Kudu ta rasa daya daga cikin fitattun matasanta masu hazaka."

Sai dai ministan bai bayyana musabbabin mutuwar Adams ba, kuma babu wata sanarwa daga hukumomin kwallon kafan kasar har kawo yanzu.

'Yan sanda sun fara bincike

'Yan sandan Afirks ta Kudu sun bayyana cewa sun fara bincike bayan an gano gawar matashin mai shekara 25 a wani gida da ke Schotschekloof, wani yanki da ke tsakiyar birnin Cape Town, cewar rahoton Sky Sports.

Kakakin 'yan sandan Western Cape, FC van Wyk, ya ce:

"Ana ci gaba da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru."

Kara karanta wannan

"Ba zan amince ba"; Wike ya gano dalilin rashin farin jininsa a wajen ma'aikata

Ya taka leda a gasar cin Kofin Duniya

Adams ya buga dukkan wasannin rukuni uku da Afrika ta Kudu ta fafata a gasar kofin duniya na 2026, amma bai buga wasan da suka sha kashi a hannun Canada a matakin Round 32.

An haife shi ne a Cape Town, inda ya fara taka leda a matakin ƙwararru a kungiyar Stellenbosch FC kafin ya koma Mamelodi Sundowns, zakarun Gasar Zakarun Nahiyar Afrika (CAF Champions League), a watan Janairun 2025.

Adams.
Dan wasan Afirka ta Kudu, Adams da wasi jami'an rundunar yan sanda Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Iyalan Adams sun sake yin rashi

Rasuwar Adams ta zo ne kasa da wata guda bayan rasuwar kakarsa, lamarin da ya kara jefa iyalansa cikin alhini da jimami.

A lokacin, ya shiga wasan da Afrika ta Kudu ta buga da Czechia duk da cewa yana cikin jimamin rashin kakarsa.

Dalilin gazawar Ronaldo a kofin duniya

A wani labarin, kun ji cewa shugaban majalisar malaman Kano kuma dan siyasa, Sheikh Ibrahim Khalil ya yi bayani game da shan kayen Cristiano Ronaldo a kofin duniya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta yi wa sojoji ƙarin lbashi mai gwaɓi don inganta walwalarsu a Najeriya

Ya bayyana cewa duk himmar Ronaldo da kwazon shi, bai kai ga inda ya ke so ba a gasar sabada rashin mataimakan da suka dace.

Saboda haka ya bayyana cewa duk gogewar mutum, basirar shi da kwarewar shi, idan bai samu abokan aiki jarirtattu ba, ba zai kai ga gaci ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262