Tashin Hankali: Mutanen Gari Sun Sassara Wata Mata da Adda har Ta Mutu a Bauchi
- Wasu da ake zargi sun kashe Hafse Ubale mai shekara 30 a Bauchi bayan sun zarge ta da maita, tare da raunata mijinta da wasu yara biyu
- Rundunar 'yan sanda ta kama mutum guda, yayin da take ci gaba da farautar wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a harin
- Kwamishinan 'yan sandan Bauchi ya yi Allah wadai da kisan, yana mai gargadin jama'a su guji ɗaukar doka a hannunsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Bauchi - Wata mata mai shekara 30, Hafse Ubale, ta rasa ranta bayan wasu da ake zargi sun kashe ta bisa zargin maita a ƙauyen Garin Malam da ke ƙaramar hukumar Gamawa a jihar Bauchi.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar 28 ga Yulin 2026 lokacin da wani da ake zargi mai suna Garba Daudu ya jagoranci wasu mutum biyu ɗauke da sanduna da adduna zuwa gidan mijin marigayiyar, Audu Sabo.
An kai hari bayan zargin maita
Ana zargin maharan sun zargi Audu Sabo da zama da matar da suke ikirarin mayya ce, kafin su kai masa hari, cewar rahoton Daily Trust.
A yayin harin, sun yi wa Audu Sabo duka, sannan suka sare Hafse Ubale da adda tare da raunata wasu 'ya'yansa biyu, Sale Audu mai shekara 12 da Yakubu Audu mai shekara 14.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Bauchi, SP Nafiu Habib, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa wani mazaunin Garin Malam mai shekara 45 ne ya kai rahoton harin ofishin 'yan sanda na Gamawa a ranar 29 ga Yuli.
Mutum guda na hannun 'yan sanda
Habib ya ce binciken farko ya nuna cewa Garba Daudu mai shekara 35 ya haɗa baki da wasu mutum biyu da aka bayyana sunayensu da Ya'u Garba da Musa wajen kai harin.
Ya ce jami'an 'yan sanda tare da haɗin gwiwar mafarauta da 'yan banga sun garzaya wurin bayan samun rahoton, inda suka kai waɗanda suka jikkata Asibitin Kwararru na Gamawa.
Likita ya tabbatar da rasuwar Hafse Ubale, sannan aka miƙa gawarta ga iyalanta domin yi mata jana'iza.
A cewarsa, ɗaya daga cikin waɗanda suka ji rauni na ci gaba da karɓar magani, yayin da aka sallami sauran biyu bayan an yi musu magani.
Kwamishinan 'yan sanda ya magantu
Habib ya ƙara da cewa an kama mutum guda da ake zargi, yayin da ake ci gaba da neman sauran mutum biyun da suka tsere bayan harin.
An miƙa shari'ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) na jihar Bauchi domin ci gaba da bincike da gurfanar da waɗanda ake zargi.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yi Allah wadai da kisan, yana mai gargadin jama'a da su guji ɗaukar doka a hannunsu ko aikata tashin hankali bisa camfi, tare da kira ga al'umma su bai wa jami'an tsaro bayanan da za su taimaka wajen cafke sauran waɗanda suka tsere.
Asali: Legit.ng

