Jihar Zamfara
Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk nada sabon gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawalle, sarautar Barden Hausa, kamar yadda sanarwa daga fadar gwamnatin jahar Zamfara ta bayyana.
A ranar Asabar 10 ga watan Agusta, akalla rayukan mutane 11 ne suka salwanta a yayin da wani mummunan hatsari ya ritsa da wasu motocin haya biyu da ya auku cikin garin Damba na karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.
Kakakin gwamnan, Yusuf Idris a wani zance da ya fitar ta hannun jaridar Premium Times ya ce, gwamnan yayi haka ne domin nuna halin tausayawa ga ‘yan fursunan. Kuma ya sake su ne domin su koma gida su yi sallah tare da iyalansu.
Abun yana matukar bani mamaki a ce ma'aikaci dake mataki (grdae level) na 16 amma albashinsa bai kai N30,000 ba, ta yaya zai yi aikinsa yadda ya kamata da irin wannan kaskantaccen albashi," a cewar Yandoto. Ya bayyana cewa fara
Jami’ar kasa da kasa dake kasar Sudan, Sudan International University, ta kulla yarjejeniya da gwamnatin jahar Zamfara domin bude rassanta a garin Gusau, da zai kunshi tsangayar ilimin likitanci don samar da kwararrun likitoci.
Cikin wata sanarwa da ta fito daga harshen mai magana da yawun gwamnan jihar, Zailani Bappah, ya ce ababen zargin wadanda ke da hannun cikin annobar ta'addanci da ta yiwa jihar daurin kama-karya za su samu 'yanci a wannan mako.
Jami’an hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC sun kai wani samame gidan tsohon gwamnan jahar Zamfara, Abdul Aziz Yari, dake garin Talatar Mafara domin gudanar da bincike.
Gwamnati jihar Zamfara ta dakatar da shugaban karamar hukumar Maradun, Ahmad Abubakar, bayan ta zarge shi da nuna halin ko in kula wajen kawo zaman lafiya a yankin. Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa...
Yan bindiga a ranar Alhamis suka sako hakimin Yan Kaba, Alhaji Buhari Ammani da iyalaansa daga cikin yarjejeniyar zaman lafiya da ake gudanarwa a jihar.
Jihar Zamfara
Samu kari