Birtaniya Ta Fallasa abin da Ya Ɓata Zaɓen Gwamnan Ekiti da Aka Yi
- Birtaniya ta yabawa INEC da jami’an tsaro kan yadda zaben gwamnan jihar Ekiti ya gudana cikin lumana tare da fadin matsalolin da ta gani
- Ofishin jakadancin Birtaniya a Najeriya ya ce an samu rahotannin matsalolin BVAS da zargin sayen kuri’u a a zaben da aka gudanar ranar Asabar
- Birtaniya ta bukaci a dauki darasi daga zaben Ekiti domin inganta sahihancin zabukan Osun da manyan zabukan shekarar 2027 da ke tafe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Babban Ofishin Jakadancin Birtaniya a Najeriya ya yabawa hukumar INEC da jami’an tsaro bisa yadda zaben gwamnan jihar Ekiti ya gudana cikin lumana.
Sai dai ofishin ya bayyana damuwa kan wasu matsaloli da ya ce an samu a yayin da aka gudanar da zaben a ranar Asabar, 20 ga Yunin 2026.

Source: Twitter
Matsalolin da aka gano a zaben Ekiti
Gwamnatin Birtaniya ta bayyana cewa, sayen kuri’u da kuma tsaiko da aka samu sakamakon matsalolin na’urar tantance masu kada kuri’a ta BVAS, sun raunana zaɓen, in ji rahoton The Cable.
Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta rahoto cewa, INEC ta ayyana Biodun Oyebanji na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan ya samu kuri’u 319,224, inda ya doke Wole Oluyede na PDP wanda ya samu kuri’u 40,543 da Dare Bejide na ADC wanda ya samu kuri’u 12,872.
Bayan kammala zaben, an samu rahotanni daga wasu rumfunan zabe kan zarge-zargen sayen kuri’u da kuma hana wasu masu zabe damar kada kuri’unsu.
Haka kuma an samu matsalolin fasaha inda wasu na’urorin BVAS suka kasa tantance wasu tsofaffin masu kada kuri’a, lamarin da ya janyo tsaiko a wasu wuraren zaben.
Ofishin jakadancin Birtaniya ya taya masu kada kuri’a a Ekiti murnar shiga zaben tare da amfani da hakkinsu na dimokuraɗiyya.
Har ila yau, ofishin ya kuma taya Gwamna Biodun Oyebanji murnar sake lashe zaben.
Abin da masu sa ido suka gani
Birtaniya ta ce zaben Ekiti shi ne babban zabe na farko da aka gudanar karkashin sabuwar Dokar Zabe ta 2026 da kuma ka’idojin da suka biyo bayanta.
Ta bayyana cewa masu sa ido nata sun gana da manyan masu ruwa da tsaki ciki har da jami’an ‘yan sanda da INEC kafin zaben domin fahimtar yadda ake aiwatar da sabuwar dokar.
Ta ce:
“Masu sa ido sun ga kyakkyawar hadin gwiwa tsakanin jami’an INEC da hukumomin tsaro a ranar zabe, wanda ya taimaka wajen tabbatar da cewa zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali.”

Source: Twitter
Kira kan inganta tsarin zabe
Ofishin ya yaba da yadda aka bai wa wasu masu kada kuri’a da ke da bukata ta musamman fifiko a wasu rumfunan zabe, amma ya ce yawancin wuraren zaben da aka ziyarta ba su dace da masu nakasa ba.
Ya kuma ce matsalolin BVAS sun janyo tsaiko wajen kada kuri’a, kuma irin wadannan matsalolin na iya rage kwarin gwiwar jama’a kan tsarin zabe.
Jaridar The Nation ta rahoto Birtaniya ta kara nuna damuwa kan katsalandan da wasu wakilan jam’iyyu suka yi da kuma sayen kuri’u a wasu wuraren zabe.
Ta ce irin wannan dabi’a na rage amincewar jama’a tare da raunana tsarin dimokuraɗiyya.
Tinubu ya taya Oyebanji murna
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya taya Gwamna Biodun Oyebanji murnar lashe zaben gwamnan jihar Ekiti, wanda aka gudanar a ranar Asabar.
Shugaban kasar na Najeriya ya ce nasarar Oyebanji ta nuna amincewar al’umma da ci gaba da manufofin gwamnatinsa a jihar Ekiti.
Yanzu da ya samu nasara, Tinubu ya bukaci gwamnan da ya hada kan dukkan ‘yan jihar tare da mayar da hankali kan ayyukan raya kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


