Ba sani ba sabo: An dakatar da shugaban karamar hukuma da Hakimi a jihar Zamfara

Ba sani ba sabo: An dakatar da shugaban karamar hukuma da Hakimi a jihar Zamfara

- Gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da shugaban karamar hukumar Maradun, Ahmad Abubakar

- Gwamnatin ta zargi Abubakar ne da nuna halin ko in kula akan neman zaman lafiya a yankin karamar hukumar

- Haka kuma gwamnatin ta dakatar da Mai Garin Boko dake masarautar Moriki, cikin karamar hukumar Zurmi, Abubakar Rafi

Gwamnati jihar Zamfara ta dakatar da shugaban karamar hukumar Maradun, Ahmad Abubakar, bayan ta zarge shi da nuna halin ko in kula wajen kawo zaman lafiya a yankin.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa gwamnan jihar Bello Matawalle ya gabatar da wani tsari na sulhu tsakaninsu da 'yan ta'adda da suka addabi jihar.

Legit.ng ta gano cewa gwamnan kuma yayi hani da kisan mutane da Fulani Makiyaya ke yi a fadin jihar.

KU KARANTA: Tirkashi: Kyawun diri na yasa wani daraktan fim kawowa a daidai lokacin da ake daukar shirin fim dani - Jaruma Juliet Ibrahim

Sanarwar dakatarwar ta fito daga bakin kakakin majalisar jihar, Nasiru Magarya jiya Laraba, bayan sammacin da aka aikawa gwamnatin jihar akan shugaban karamar hukumar.

Wanda suka aika sammacin sun zargi shugaban karamar hukumar da hada baki da 'yan banga wajen tilasta Fulani Makiyaya akan su bar yankin karamar hukumar ta Maradun, bayan shi kuma gwamnan jihar ya bayyana cewa a kyale Fulani Makiyaya su shiga duk inda suke so a fadin jihar.

Bayan haka kuma, gwamnatin jihar ta dakatar da Abubakar Rafi, Mai Garin Boko dake karkashin masarautar Moriki cikin karamar hukumar Zurmi.

An dakatar da Mai Garin ne bayan zargin da ake yi masa na kwace wasu gonaki na talakawansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel