Matawalle ya sanar da sunan sabon shugaban ma’aikatan jahar Zamfara

Matawalle ya sanar da sunan sabon shugaban ma’aikatan jahar Zamfara

Gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawallen Maradun ya amince da nadin Alhaji Kabiru Balarabe a matsayin sabon shugaban ma’aikatan gwamnatin jahar Zamfara, inji rahoton jaridar Premium Times.

Babban daraktan watsa labaru na fadar gwamnatin jahar, Yusuf Idris ne ya sanar da haka a ranar Lahadi, 18 ga watan Agusta, inda yace nadin Kabiru wannan mukami ya fara ne nan take.

KU KARANTA: Jami’ar Wudil ta aika sunayen hazikan dalibai 296 ga Dangote domin ya basu aikin yi

Gwamna Matawalle ya nada Kabiru ne don maye gurbin Alhaji Mujitaba Isah wanda ya yi ritaya daga aiki a kwanakin baya, gwamnan ya taya Mujitaba murnar ajiye aiki lafiya, tare da taya shi fatan alheri a gaba.

Sa’annan gwamnan ya taya sabon shugaban ma’aikatan murna, inda ya nemi ya jajirce wajen gyara tsara aikin gwamnati a jahar Zamfara, ta yadda za ta zamo madubin dubawa ga sauran jahohin Najeriya.

Shi dai sabon shugaban ma’aikatan jahar Zamfara an haifeshi ne a ranar 15 ga watan Maris na shekarar 1966, kuma ya yi karatun digiri a jami’ar Usmanu Danfodiyo dake Sakkwato, inda ya fara aiki a ranar 21 ga watan Agustan 1991 a ofishin gwamnan mulkin Soja na jahar Sakkwato.

Ya rike mukamai daban daban da suka hada da sakataren tsohon shugaban kasa Aliyu Usman Shehu Shagari daga 1993 zuwa 1996, wakilin jahar Sakkwato a kwamitin mika mulki ga farar hula a zamanin gwamnatin soja ta janar Ibrahim Badamasi Babangida, har ma ya taba zama babban sakatare a Sakkwato.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel