Tsaro: An Saki Sunayen Mutanen da aka Kama da Buhuna 47 na Kayan Sojoji
- Rundunar ‘yan sanda a jihar Lagos ta kama buhuna kusan 50 na kayan sojoji da kwalaye kusan 100 na abubuwan da ake zargi miyagun ƙwayoyi ne
- Rahoto ya nuna cewa an kama mutane uku da ake zargi da hannu a safarar kayayyakin da aka gano cikin wata babbar motar ɗaukar kaya
- Binciken farko da 'yan sanda suka gudanar ya nuna cewa ana zargin an shirya kai kayayyakin sojojin ne zuwa yankin Kudu maso Gabas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Legas - Rundunar ‘yan sandan jihar Lagos ta kama buhunan kayan sojoji da kwalayen wasu kayayyakin da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne.
An kama kayayyakin ne a wani samame da jami'an 'yan sanda suka gudanar bisa bayanan sirri a yankin Surulere na jihar Legas.

Kara karanta wannan
An tsinci gawar babban malamin addini cikin wani yanayi a ɗakin otal a jihar Ondo

Source: Twitter
Sunayen wadanda aka kama
Punch ta rahoto cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Fatai Tijani, ya bayyana wa manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Ikeja cewa an kama mutane uku da ake zargi da hannu a lamarin.
Ya ce jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane na rundunar ne suka kama waɗanda ake zargin a daren ranar Asabar da ta gabata.
An bayyana sunayensu da Chinedu David mai shekara 29, Ezeagwu Chukwuma mai shekara 38, da Ifeanyi Ogbeanyi mai shekara 45.
Yawan kayan sojoji da aka kama
A cewar kwamishinan, an kama mutanen ne tare da wata babbar mota mai amfani da dizal wadda ba ta da rajista, dauke da buhuna 47 na kayan sojoji da kuma kwalaye 80 na kayayyakin da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne.
Ya ce:
“Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Lagos da ke sashen yaƙi da garkuwa da mutane, bayan gudanar da aiki bisa bayanan sirri, sun samu gagarumar nasara ta hanyar kama mutane uku da ake zargi.
“Har ila yau, an kwato wata motar MAN mai amfani da dizal da ba ta da rajista, wadda ke ɗauke da buhuna 47 na kayan sojoji da kwalaye 80 na kayayyakin da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne.”

Source: Twitter
Ina za a kai kayayyakin?
Premium Times ta rahoto cewa kwamishinan ya ce binciken farko ya nuna cewa ana zargin an shirya jigilar kayan sojojin ne zuwa yankin Kudu maso Gabashin ƙasar nan.
Ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano inda aka samo kayan, masu su, da kuma waɗanda aka shirya kai wa, tare da gano sauran mutanen da ke da hannu a lamarin.
An sace iyalan shugaban APC
A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu 'yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kama iyalan shugaban jam'iyyar APC a jihar Kebbi.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan ta'addan sun shiga gidan shi ne da ke karamar hukumar Yauri suka tafi da matar shugaban da ɗan shi.
Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da kama iyalan shugaban jam'iyyar tare da cewa an bazama cikin daji neman masu garkuwa da su.
Asali: Legit.ng
