Afuwa: Gwamnan Zamfara ya sallami fulanin daji 100 daga dauri

Afuwa: Gwamnan Zamfara ya sallami fulanin daji 100 daga dauri

A yayin ci gaba da zage dantse wajen tabbatar da sulhu, gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle, ya kudiri aniyar yin afuwa tare da gafarta wa fursunonin 'yan banga da kuma fulani dake tsare a gidajen cin sarka.

Cikin wata sanarwa da ta fito daga harshen mai magana da yawun gwamnan jihar, Zailani Bappah, ya ce ababen zargin wadanda ke da hannun cikin annobar ta'addanci da ta yiwa jihar daurin kama-karya za su samu 'yanci a wannan mako.

A cewar Malam Zailani, wannan hukunci ya fito ne daga bakin gwamna Matawalle bayan wani zama na musamman da ya gudana tare da jagororin Fulani masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da sulhu a tsakanin gwamnati da kuma 'yan uwansu da ke rike da makamai cikin dajika a jihar.

Tuni dai 'yan bindiga suka fara sassauta tutar ta'addanci bayan wani taro da aka gudanar cikin watan Yulin da ya gabata a tsakanin mahukunta da kuma shugabannin 'yan bindigar a karamar hukumar Birnin Magaji.

Hakan ya biyo bayan yunkurin sabuwar gwamnatin jihar ne na samar da zaman lafiya bayan dubunnan mutane sun rasa rayukansu a sanadiyar ci gaba da aukuwar hare-hare tsawon shekaru da dama da ya ki ci ya ki cinye wa.

KARANTA KUMA: Kaso 40% na yaran jihar Yobe ba sa zuwa makaranta

A wani rahoto da jaridar BBC Hausa ta wallafa a watan Yulin da ya gabata, gwamnan Zamfara Matawalle, ya ce sulhu a tsakanin 'yan banga da Fulani ya fara nasara wajen kawo karshen rikicin da ya addabi jihar.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, an dade na rikici a jihar Zamfara wanda ya yi sanadiyar mutuwa gami da sace mutane da kuma dabbobi da dama.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel