Ekiti da Sauran Jihohi 4 da APC Ta Lashe a Mulkin Shugaba Tinubu

Ekiti da Sauran Jihohi 4 da APC Ta Lashe a Mulkin Shugaba Tinubu

FCT, Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta samu nasararori a zabubbuka da dama da aka gudanar a mulkin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Daga cikin zabubbukan da APC ta samu nasara ciki da na gwamnoni a wasu jihohin tarayyar Najeriya.

APC ta samu nasara a zaben gwamna a wasu jihohi
Gwamna Biodun Oyebanji na Ekiti, Gwamna Monday Okpebholo na Edo da Gwamna Hope Uzodimma na Imo Hoto: Biodun Oyebanji, Sen Monday Okpebholo, Hope Uzodimma
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro wasu jihohi da jam'iyar APC ta lashe zaben gwamna tun bayan hawan shugaban kasa, Bola Tinubu, kan kujerar mulki.

Jam'iyyar APC ta kara karfi a Najeriya

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta na da gwamnoni a mafi yawan jihohin Najeriya, wanda hakan ya nuna karfin da take da shi.

Bayan zaben shekarar 2023, jam'iyyar APC na da gwamnoni 21 a jihohin Najeriya, amma ya zuwa shekarar 2026, adadinsu ya karu zuwa 30.

Wasu daga cikin wadannan gwamonin sun lashe zabe ne a karkashin inuwar jam'iyyar APC, yayin da wasu kuwa sauya sheka suka yi daga jam'iyyun adawa.

Kara karanta wannan

Siyasar Pantami ta kara karfi a Gombe da tsohon hadimin gwamna ya koma PDP

Jihohin da APC ta lashe a mulkin Tinubu

Tun bayan hawan Shugaba Bola Tinubu kan kujerar mulki, an gudanar da zabubbukan gwamnoni a jihohi shida na Najeriya.

Daga cikin wadannan jihohin, jam'iyyar APC ta samu nasara a jihohi biyar, yayin da ta yi rashin nasara a jiha daya tilo.

Ga jerin jihohin da APC ta yi nasara:

1. Jihar Ekiti

Jam'iyyar APC ta samu nasarar lashe zaben gwamnan jihar Ekiti da aka gudanar a ranar Asabar, 20 ga watan Yunin shekarar 2026.

Hukumar zabe ta INEC ta ayyana gwamna mai ci na Ekiti, Biodun Oyebanji na jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar, rahoton The Guardian ya nuna hakan.

Biodun Oyebanji ya yi nasara a zaben gwamnan Ekiti
Gwamna Biodun Oyebanji bayan kada kuri'arsa a zaben gwamnan Ekiti Hoto: Biodun Oyebanji
Source: Twitter

Biodun Oyebanji ya samu jimillar ƙuri’u 319,224, wanda ya ba shi nasara a kan manyan abokan hamayyarsa a zaɓen da aka gudanar a ƙananan hukumomi 16.

2. Jihar Ondo

A ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban 2024, hukumar zabe mai zaman kanra ta kasa (INEC), ta gudanar da zaben gwamna a jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Ekiti: Dalilan da suka sanya PDP da ADC kasa nasara kan APC

Lucky Aiyedatiwa ya yi nasara a zaben gwamnan Ondo
Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo Hoto: Rt Hon Lucky Aiyedatiwa
Source: Facebook

Hukumar zabe ta INEC ta tabbatar da Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

Gwamna Aiyedatiwa na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 366,781 yayin da PDP mai adawa ta damu kuri'u 117,845, cewar rahoton Channels TV.

3. Jihar Edo

Hukumar INEC ta ayyana ɗan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Edo, Monday Okpebholo, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan da aka gudanar ranar Asabar, 21 ga watan Satumba, 2024.

Gwamna Monday Okpebhola ya samu nasara a Edo
Gwamna Monday Okpebhola na Edo a wajen taron APC Hoto: Sen Monday Okpebholo
Source: Facebook

A cewar rahoton jaridar TheCable, babban jami'in tattara sakamakon zaɓen ya ce Okpebholo ya samu ƙuri'u 291,667 inda ya doke ɗan takarar jam'iyyar PDP, Asue Ighodalo, wanda ya samu ƙuri'u 247,274.

Sakamakon ya nuna cewa Okpebholo ya yi nasara a ƙananan hukumomi 11 a jihar, yayin da Ighodalo ya yi nasara a ƙananan hukumomi bakwai, wannan ya kawo karshen PDP mai mulki a Edo.

4. Jihar Imo

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya lashe zaben gwamnan da hukumar zabe ta INEC ta gudanar a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamban 2023.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Ekiti: APC ta aika sako ga Oyebanji bayan samun tazarce

Babban jami'in tattara sakamakon zaɓe na INEC, Abayomi Sunday, ya ce ɗan takarar na APC ya samu ƙuri'u 540,308 inda ya doke babban mai ƙalubalantarsa na PDP, Samuel Anyanwu, wanda ya samu ƙuri'u 71,503, Premium Times ta kawo labarin.

Hope Uzodinma ya samu tazarce a jihar Imo
Gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma Hoto: Hope Uzodinma
Source: Facebook

'Dan takarar jam'iyyar LP Athan Achonu, ya zo na uku da ƙuri'u 64,081. Babu ɗaya daga cikin sauran 'yan takara 15 da ya samun ƙuri'un da suka kai 10,000.

Nasarar ta sanya Gwamna Uzodinma ya samu tazarce a jihar wadda ke a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

5. Jihar Kogi

Hukumar INEC ta sanar da ɗan takarar gwamna na jam'iyyar APC, Usman Ododo, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kogi na ranar 11 ga watan Nuwamban 2023.

Ahmed Ododo ya samu nasara a zaben gwamnan Kogi
Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo Hoto: Alhaji Ahmed Usman Ododo
Source: Facebook

The Punch ta kawo rahoto cewa Ahmed Usman Ododo ya samu nasara ne da ƙuri'u 446,237, inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Murtala Ajaka na jam'iyyar SDP wanda ya samu ƙuri'u 259,052.

Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben, Sanata Dino Melaye ya samu ƙuri'u 46,362, jaridar The Cable ta kawo rahoton.

APC ta samu nasara a zaben Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar jam'iyyar a zaben cike gurbi da aka gudanar a jihar Kano a ranar Asabar, 20 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

'Za ta karewa Tinubu a 2027,' Momodu ya fadi yadda Atiku zai kifar da APC

Hukumar INEC ta ayyana Rabiu Shuaibu, ɗan takarar jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaɓen na mazabar Dawakin Kudu/Warawa.

Rabiu Shuaibu na APC ya samu ƙuri’u 35,356, Lawal Garba Haruna na APM ya samu ƙuri’u 268, yayin da Abubakar Yahya Muhammad na jam’iyyar LP ya samu ƙuri’u 98.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng