Zamfara: Yan bindiga sun saki Hakimin Yan Kaba da iyalansa

Zamfara: Yan bindiga sun saki Hakimin Yan Kaba da iyalansa

Yan bindiga a ranar Alhamis suka sako hakimin Yan Kaba, Alhaji Buhari Ammani da iyalaansa daga cikin yarjejeniyar zaman lafiya da ake gudanarwa a jihar.

Yan bindigan sun sace hakimin Yan Kaba a karamar hukumar Kaura Namoda da iyalansa watanni uku da suka gabata a lokacin da suka kai ma kauyen hari.

Yayin da yake gabatar da wadanda aka sace ga gwamna Bello Mutawalle, babban hadimin Gwamna, Abubakar Mohammed Dauran yace an sace hakimin ne da iyalansa watanni uku da suka gabata.

Yace yan bindiga sun amince cewa zasu sakar ma gwamnatin jihar sub a tare da wani dalili ba saboda ganin da suka yi cewa akwai kamshin gaskiya cikin shiri na zaman lafiyan da Gwamnan yazo da shi.

Yayinda yake mayar da martani akan cigaban, Gwamna Mutawalle ya sha alwashin cewa zai hukunta duk wani ko wata kungiya da ke kokarin kawo tangarda ga shirin zaman lafiyar da gwamnatinsa ta kawo jihar.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Gwamna Yahaya Bello na farautar rayuwa na – Mataimakin gwamna

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, zai jagoranci wata tawaga ta manyan jami’an yan sanda zuwa wajen wani ganawa tare da wasu gwamnoni a cikin kokarin magance matsalar rashin tsaro da ake fuskanta a yankunan kasar.

Majiyarmu ta ruwaito cewa za a yi ganawar ne a yau Alhamis, 1 ga watan Agusta a gidan gwamnatin jihar Katsina.

Wadanda ake sanya ran za su halarci ganawar sune gwamnoni, kwamishinonin yan sanda daga jihohin arewa maso yamma, wato Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto da kuma Zamfara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel