Hatsarin mota ya hallaka mutane 11 a Zamfara

Hatsarin mota ya hallaka mutane 11 a Zamfara

A ranar Asabar 10 ga watan Agusta, akalla rayukan mutane 11 ne suka salwanta a yayin da wani mummunan hatsari ya ritsa da wasu motocin haya biyu da ya auku cikin garin Damba na karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.

Gwamnan jihar Muhammad Bello Mutawalle wanda ya isa harabar wannan mummunan tsautsayi jim kadan bayan ya auku, ya bayar gudunmuwa wajen taimakon wadanda suka jikkata kamar yadda sakataren sadarwa na fadar gwamnatin Zamfara, Yusuf Idris ya bayar da shaida.

Alhaji Idris ya ce aukuwar mummunan tsautsayi da misalin karfe 4.00 na Yammaci ya faru ne a sanadiyar tsala gudu da daya daga cikin motocin biyu ke yi wanda ya wuce misali gami da sabawa ka'aidar tuki.

Kamar yadda gwamna Mutawalle ya bayar da umarni, an garzaya da gawawwakin wadanda suka riga mu gidan gaskiya zuwa babbar cibiyar lafiya ta gwamnatin Tarayya wato FMC Federal Medical Center Gusau inda aka killace su.

Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnatin jihar Zamfara za ta dauki nauyin duk wata dawainiya da za a yi da wadanda suka riga mu gidan gaskiya har zuwa sanya su a makwanci a matsayin wani yunkuri na bayar da gudunmuwarta ga 'yan uwan wadanda ibtila'in ya auku a kansu.

KARANTA KUMA: Zaben kananan hukumomi: PDP ta lashe dukkanin kujeru 8 a jihar Bayelsa

Legit.ng ta cewa, tsautsayi da Hausa kan ce ba ya wuce ranarsa ya sanya ajali ya yiwa fasinjoji 10 da kuma direbansu yankan kauna yayin da suke kan hanyar dawowa daga babban birnin kasar nan na Tarayya Abuja.

Mutane 9 da ajali ya yiwa yankan kauna sun kasance mutanen garin Jangeru na karamar hukumar Shinkafi yayin da direban motar ya kasance mutumin wani kauye daga karamar hukumar Kauran Namoda.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel