Bola Tinubu Ya Nada Tsohon VC a matsayin Shugaban Hukumar NUC ta Najeriya
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada tsohon shugaban jami'ar UNILAG, Farfesa Oluwatoyin Ogundipe, a matsayin shugaban hukumar NUC
- Farfesa Ogundipe ya maye gurbin Olufemi Aina, wanda ya yi murabus kasa da shekara guda bayan nadinsa a mukamin
- Gwamnatin tarayyya na fatan sabon shugaban NUC zai inganta tsarin jami'o'in Najeriya ta yadda za su yi gogayya a duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin tsohon shugaban Jami'ar Legas (UNILAG), Farfesa Oluwatoyin Ogundipe, a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na Hukumar Kula da Jami'o'i ta Kasa (NUC).
Mai ba shugaban kasa shawara kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Source: Twitter
A cewar sanarwar da Onanuga ya wallafa a shafinsa na X, Farfesa Ogundipe ya maye gurbin Olufemi Aina, wanda ya yi murabus daga mukaminsa kasa da shekara guda bayan nada shi.
Aikin da aka dorawa shugaban NUC
Onanuga ya ce sabon shugaban zai jagoranci hukumar NUC da ke kula da tsarin jami'o'in Najeriya tare da mayar da hankali kan samar da kudade da kara wa jami'o'i gasa a matakin duniya.
Ya ce:
“An yi wannan nadin ne domin bunkasa inganci, fadada damar samun ilimi da kuma kare martabar bangaren ilimi a Najeriya.”
Tinubu ya fadi abin da yake tsammani
Sanarwar ta kara da cewa Shugaba Tinubu na sa ran Farfesa Ogundipe zai samar da nagartaccen shugabanci a NUC tare da tabbatar da ɗaga martabar jami'o'in Najeriya daidai da manufofin shirin Renewed Hope Agenda.
Farfesa Ogundipe ya rike kujerar shugaban Jami'ar Legas daga shekarar 2017 zuwa 2022, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Takaitaccen bayani kan Ogundupe
Ya samu digirin digirgir (PhD) a fannin ilimin tsirrai daga Jami'ar Obafemi Awolowo (OAU), sannan ya yi MBA a Jami'ar Legas.
Farfesan, wanda ya kware a fannin ilimin tsirrai, ya yi bincike kan fannoni da suka hada da,Molecular Plant Taxonomy, Biosystematics,Ethnobotany, Cytogenetics, Forensic Botany, da kare muhalli da albarkatun kasa.
Onanuga ya bayyana cewa malamin mai shekaru 66 a yanzu yana matsayin shugaban majalisar gudanarwa na Jami'ar Redeemer’s da ke Ede a jihar Osun.

Source: Twitter
Har ila yau, Oluwatoyin Ogundipe mamba ne na kungiyoyi masu yawa na masana kimiyya, ciki har da, Nigerian Academy of Science, Linnaean Society of London da Royal Society of Biology
Nadin na daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ke dauka domin karfafa tsarin ilimin jami'o'i da inganta nagartar ilimi a Najeriya.
Tinubu ya tsawaita wa'adin shugaban NCS
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ƙara tsawaita wa’adin aikin shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), Adewale Adeniyi, da watanni shida.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce sabon ƙarin wa’adin na watanni shida, wanda zai ƙare a watan Fabrairun 2027, zai ba Adeniyi damar ƙarfafa aiwatar da tsare-tsaren gwamnati tare da tabbatar da sauyin shugabanci cikin tsari.
Asali: Legit.ng

