Talauci ya jefa wata budurwa cikin mawuyacin hali bayan saurayinta ya kasa biyan sadakin aurenta

Talauci ya jefa wata budurwa cikin mawuyacin hali bayan saurayinta ya kasa biyan sadakin aurenta

Wata budurwa yar shekara 17 ta dauki wani mummunan mataki a kanta ta hanyar banka ma kanta wuta bayan ta bulbula fetir a jikinta a dalilin cewa saurayin da take soyayya da shi ya gagara biyan sadakin aurenta, wanda mahaifinta ya yanka masa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wannan yarinya mai suna Aisha da take zaune a unguwar Albarkawa cikin garin Gusau tare da iyayenta ta yi kokarin kashe kanta ne a ranar Lahadi, sakamakon tsananin talauci dake damun saurayinta, Umar, da har ta kai ba zai iya biyan N17,000 sadakin aurenta ba.

KU KARANTA: Direbobin haya sun koka da dawowar masu garkuwa da mutane kan hanyar Kaduna zuwa Abuja

Majiyar Legit.ng ta ruwaito iyayen Aisha sun gayyaci Umar domin ya fito a fara shirye shiryen aure, amma yace musu gaskiya ba zai iya fitowa ba sakamakon bashi N17,000 da suka yanka masa a matsayin sadakin auren Aisha.

“Daga nan sai ta dauko wani galan cike da fetur ta bulbule shi a jikinta, sa’annan ta kyasta ashana, kafin a ankara ta kama ci da wuta. Kafin nan kanwarta ta yi ta yi ta hanata kyasta ashanar ta hanyar buge hannunta, amma sai Aisha ta sake kunna wani.

“Da kanwar ta gaji ne sai ta ruga waje a guje tana neman taimako, a haka ta ci karo da wasu samari da suka rugo cikin gidan, suka samu nasarar kashe ta, ganin haka mahaifin yace gaskiya ba zai iya kaita asibiti ba sakamakon N750 ya mallaka gaba da baya!” Inji makwabcinsu.

A yanzu haka dai Aisha tana gida tana samun kulawa da magungunan gargajiya. Sai dai kaakakin Yansandan jahar Zamfara, Muhammadu Shehu ya bayyana rashin masaniya game da aukuwar lamarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel