Gwamnatin jihar Zamfara za ta fara biyan N30,000 a matsayin mafi karancin albashi

Gwamnatin jihar Zamfara za ta fara biyan N30,000 a matsayin mafi karancin albashi

Shugaban ma'aikatar kula da aiyukan kananan hukumomin jihar Zamfara, Alhaji Mallami Yandoto, ya ce gwamnatin jihar zata fara biyan ma'aikatan jihar sabon mafi karancin albashi na N30,000 a wata.

Shugaban ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin wata tattaunawa da ya yi da kamfanin dillancin labari na kasa (NAN) a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Yandoto ya bayyana cewa ko kadan baya jin dadin yadda ma'aikatan kananan hukumomin jihar ke karbar albashin da ya gaza N18,000 a wata.

"Abun yana matukar bani mamaki a ce ma'aikaci dake mataki (grdae level) na 16 amma albashinsa bai kai N30,000 ba, ta yaya zai yi aikinsa yadda ya kamata da irin wannan kaskantaccen albashi," a cewar Yandoto.

Ya bayyana cewa fara biyan ma'aikata kananan hukumomin jihar albashin N30,000 zai kara musu himma wajen sauken nauyin da aka dora musu.

DUBA WANNAN: Shugaban majalisar dattijai ya fitar da sabon hotonsa a hukumance da kuma lakabin da za ke kiransa da shi

A cewarsa, karin albashin zai sa ma'aikatan suke zuwa wurin aiki a kan lokaci da kuma daukan aikinsu da muhimmanci.

"Daga yanzu ma'aikatar kula da kananan hukumomi zata dauki nauyin biyan albashin ma'aikatan kananan hukumomi da kuma sa ido a kan aiyukansu da kula da cigabansu," a cewarsa.

Ya ce daga yanzu ma'aikatarsa ba zata nade hannayenta ta zuba ido tana kallon 'yan siyasa na cin zalin ma'aikatan kananan hukumomi ba.

Yandoto ya jadda aniyar ma'aikatarsa na daukan nauyin ma'aikatan kananan hukumomi da ke son zuwa karo karatu a makarantun fadin kasar nan, da ma ketare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel