Jami’ar kasar Sudan za ta bude tsangayar ilimin likitanci a jahar Zamfara
Jami’ar kasa da kasa dake kasar Sudan, Sudan International University, ta kulla yarjejeniya da gwamnatin jahar Zamfara domin bude rassanta a garin Gusau, da zai kunshi tsangayar ilimin likitanci don samar da kwararrun likitoci.
Kaakakin gwamnan jahar Zamfara, Gwamna Bello Matawalle, Malam Yusuf Idris ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Talata, 6 ga watan Agusta, inda yace an cimma wannan yarjejeniya ce tsakanin gwamna Matawalle da shugaban jami’ar, Farfesa Bakri Osman Saeed a garin Gusau.
KU KARANTA: Gwamna Abubakar ya shiga sahun musulmai masu gudanar da aikin Hajji a Saudiyya
Amma kaakakin yace za’a gudanar da yarjejeniyar a hukumance bayan bukukuwan babbar Sallah, ya cigaba da cewa tsangayar za ta baiwa da daliban jahar Zamfara masu sha’awar karatun likitanci gurbi a cikinta.
“Wannan shawara na baiwa bangaren ilimi fifiko, mun daukeshi ne don cimma muradunmu domin kuwa babu wani cigaba da za’a samu ba tare da ilimi ba. Gwamnati za ta samar da fili ga jami’ar, jami’ar kuma za ta gina dukkanin gine gine da ake bukata.” Inji shi.
Sanarwar ta cigaba da cewa jami’ar Sudan ta baiwa daliban jahar Zamfara da dama guraben karatu a can kasar Sudan, amma burin Gwamna Matawalle shine samar da sabbin likitoci 3000 a jahar kafin karshen wa’adin mulkinsa.
Daga karshe shugaban jami’ar, Farfesa Bakri ya shaida ma Gwamna Matawalle cewa sun zo jahar Zamfara ne domin tayashi murnar samun nasarar zama gwamna, sa’annan sun yi alkawarin zaftare wani kaso na kudin makaranta ga daliban jahar Zamfara.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng