Tofa: Gwamna Makinde Ya Ayyana Dokar Hana Fita Ta Awa 16 a Kananan Hukumomi 10

Tofa: Gwamna Makinde Ya Ayyana Dokar Hana Fita Ta Awa 16 a Kananan Hukumomi 10

  • Gwamnatin Oyo ta ayyana dokar hana fita ta sa’o’i 16 a kananan hukumomi 10, wadda za ta rika aiki daga karfe 4:00 na yamma zuwa 8:00 na safe
  • Matakin ya shafi yankunan da ke kewaye da tsohon gandun dajin kasa na Oyo, saboda matsalolin tsaro da ke kara karuwa a yankin
  • Gwamnatin jihar Oyo ta bukaci mazauna yankunan da su bi umarnin tare da bada hadin kai ga jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiyarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Oyo - Gwamnatin jihar Oyo ta sanar da ayyana dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 16 a kananan hukumomi 10 na jihar.

Gwamnatin ta sanya dokar ne sakamakon matsalolin tsaro da ake fuskanta a yankunan da ke makwabtaka da tsohuwar gandun daji ta kasa da ke jihar.

Gwamna Seyi Makinde ta ayyana dokar hana fita a Oyo
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo a wani taron majalisar zartarwa. Hoto: @seyimakinde
Source: Facebook

An sanya dokar hana fita a Oyo

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamna ya rage albashin ma'aikata suna sa ran za a kara masu

Gwamna Seyi Makinde ne ya amince da matakin, wanda zai fara aiki daga ranar Laraba, 24 ga Yuni, 2026, tare da fara aiki daga karfe 4:00 na yamma zuwa 8:00 na safiyar kowace rana, in ji rahoton Vanguard.

An bayyana cewa matakin zai fara aiki na tsawon sa’o’i 48, kafin a sake duba halin da ake ciki, don ganin ko akwai bukatar a sassauta ko a a.

A cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jiha, Farfesa Musibau Babatunde, ya fitar, gwamnati ta bayyana cewa matakin ya zama dole domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a a yankunan da abin ya shafa.

Sanarwar ta ce yankunan da ke kusa da tsohon gandun dajin kasa na Oyo ne suka fi fuskantar matsalolin tsaro, lamarin da ya sa aka dauki matakin gaggawa na takaita zirga-zirga a lokacin dare da yamma.

Yankunan da dokar ta shafa

A cewar gwamnatin jihar, kananan hukumomi 10 da dokar ta shafa sun hada da:

  • Oriire (Ikoyi-Ile)
  • Orelope (Igboho)
  • Irepo (Kisi)
  • Saki West (Saki)
  • Saki East (Ago-Amodu)
  • Atisbo (Tede/Ago-Are)
  • Itesiwaju (Otu)
  • Iseyin (Iseyin)
  • Olorunsogo (Igbeti)
  • Atiba (Offa-Meta, Oyo)
Matsalar tsaro ta sanya an ayyana dokar hana fita ta sa'o'i 16 a jihar Oyo.
Taswirar jihar Oyo, inda aka ayyana dokar hana fita ta awanni 16. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kira ga mazauna yankunan

Gwamnatin Oyo ta bukaci mazauna yankunan da abin ya shafa su bi umarnin dokar hana fita ba tare da karya doka ba. Ta kuma ce jami’an tsaro za su kasance a wurare daban-daban domin tabbatar da bin umarnin.

Kara karanta wannan

Sowore: Kotu ta bada umarnin tsare dan takarar shugaban kasa a gidan yarin Kuje

Haka kuma gwamnati ta bayyana cewa za a ci gaba da duba halin tsaro bayan karewar wa’adin farko na sa’o’i 48, sannan za a yanke shawara kan matakin da zai biyo baya, in ji rahoton Tribune.

Masu sharhi kan al’amuran tsaro sun bayyana cewa wannan mataki na daga cikin kokarin gwamnati na dakile yawaitar matsalolin tsaro a yankunan da ke da muhimmanci a fannin gandun daji da wuraren kariya a Oyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com