Tubabbun 'yan daban daji suna taimaka mana yakar ta'addanci a Zamfara - Matawalle

Tubabbun 'yan daban daji suna taimaka mana yakar ta'addanci a Zamfara - Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle, ya yi karin haske kan nasarorin da ake samu ta hanyar ci gaba da sulhun da ya ce ana yi tsakanin 'yan bindiga da Fulani domin kawo karshen rikicin da ya addabi jihar.

An dade ana zaman fargaba a jihar Zamfara a sakamakon rikicin 'yan daban daji da kuma hare-haren Fulani da ya ki ci ya ki cinyewa, lamarin da ya salwantar da rayukan mutane da dama gami da asarar dukiya musamman dabbobin kiwo masu tarin yawa.

Amma gwamnan ya zuwa yanzu ya ce tubabbun 'yan daban daji da suka ajiye makaman yaki na taimakawa jami'an tsaro a fagen yaki da ta'addanci a jihar da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Gwamna Matawalle ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin gabatar da jawabai na son barka a wani taron kwanaki uku na horo da rundunar dakarun sojin kasa ta Najeriya ta ke gudanarwa a babban birnin jihar na Gusau.

Ya ce wannan nasara ta biyo bayan shirin yin sasanci da tabbatar da sulhu da gwamnatinsa ta assasa na samar da zaman lafiya, ya sanya tubabbun 'yan bindiga na bayar da gudunmuwa ta kawo karshen tarzomar da ta mamaye wasu yankuna a jihar.

Gwamnan ya jaddada cewa zai ci gaba da ribatar tsarin sulhu da neman sasanci a tsakanin sa da dukkanin masu tayar da zaune tsaye a jihar, lamarin da ya ke kira ga sauran gwamnoni su ribata a matsayin mafificiyar hanya ta wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma.

KARANTA KUMA: Muna fuskantar kalubale na yawan jama'a a Najeriya - Buhari

Ya kuma sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta kafa burtalai na kiwo da Rugar Fulani domin makiyaya a jihar sa, inda ya ke neman agajin gwamnatin tarayya da ta kawo masa dauki wajen tabbatuwar wannan lamari.

Hakazalika, gwamnan ya yabawa rundunar dakarun sojin kasa da ma sauran hukumomin tsaro dangane da yadda suke ci gaba da sadaukar da kai da tsayuwar daka wajen yakar miyagun ababe masu ta'ada a ban kasa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel