Babbar sallah: Gwamnan Zamfara ya yiwa ‘yan fursuna 150 afuwa

Babbar sallah: Gwamnan Zamfara ya yiwa ‘yan fursuna 150 afuwa

-Matawallen Maradun ya yiwa 'yan fursuna 150 afuwa a gidan yarin jihar Zamfara

-Kakakin gwamnan Yusuf Idris ne ya fitar da wannan labari a wata hira da manema labarai ranar Juma'a 9 ga watan Agusta

-Gwamnan ya bada kyautar shanu da raguna ga sauran wadanda suka rage a gidan yari domin su yi sallah cikin farin ciki

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle a ranar Juma’a ya yiwa ‘yan fursuna 150 wadanda ke tsare a Gusau Maximum Security Prison afuwa.

Kakakin gwamnan, Yusuf Idris a wani zance da ya fitar ta hannun jaridar Premium Times ya ce, gwamnan yayi haka ne domin nuna halin tausayawa ga ‘yan fursunan. Kuma ya sake su ne domin su koma gida su yi sallah tare da iyalansu.

KU KARANTA:Yanzu-yanzu: Gwamna Matawalle ya tsige Sarkin Maru

Daga cikin wadanda aka yiwa afuwan akwai mutum biyar da aka yankewa hukuncin kisa, biyar dake karkashin daurin rai da rai da kuma mata masu shayarwa su tara.

Bugu da kari, akwai mutum 30 wadanda ke tsare bisa laifuka daban-daban, 60 dake jiran hukuncin kotu da kuma 41 wadanda suka samu alfarmar haddace Al-kur’ani mai girma a gidan yarin.

‘Yan gidan kason dake da nakasa da kuma wadanda suka haura shekara 20 a gidan yarin suna cikin wadanda aka yiwa afuwa.

Haka zalika, an nemi wadanda aka yiwa afuwan da su dauki wannan al’amari a matsayin abinda zai kasance sabon shafi cikin rayuwarsu domin gujewa sake aikata wani abin da zai maida su gidan yarin.

Har ila yau, gwamnan ya bada kyautar shanu biyar, buhun shinkafa 100, raguna biyar, magunguna da kuma sauran kayan abinci ga sauran ‘yan gidan yari domin suyi sallah babba cikin farin ciki, kamar yadda zance ya sanar da mu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel