Barden Hausa: Sabon sarautar da sarkin Daura ya nada Gwamna Matawalle

Barden Hausa: Sabon sarautar da sarkin Daura ya nada Gwamna Matawalle

Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk nada sabon gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawalle, sarautar Barden Hausa, kamar yadda sanarwa daga fadar gwamnatin jahar Zamfara ta bayyana.

Kaakakin gwamnan, Yusuf Idris ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 15 ga watan Agusta a gari Gusau, inda yace gwamnan da kansa ya amshi takardar nadin sarautar daga hannun Sarkin yayin ziyarar daya kai masa a fadarsa dake Daura.

KU KARANTA: Yadda Buhari ya shiga cikin ruwan sama yayin kaddamar da wasu sabbin hanyoyi 2 a Katsina

Barden Hausa: Sabon sarautar da sarkin Daura ya nada Gwamna Matawalle
Barden Hausa: Sabon sarautar da sarkin Daura ya nada Gwamna Matawalle
Asali: Facebook

Wasikar nadin sarautar ta bayyana cewa Sarkin ya ga dacewar bayar da sarautar ga Matawalle ne bisa namijin kokarin da yake yi wajen dawo da zaman lafiya a jahar Zamfara, da ma sauran sassan Arewacin Najeriya.

“Sarkin Daura ya bayyana farin cikinsa da goyon bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake bawa Gwamna Matawalle wajen magance matsalar tsaro a jahar Zamfara duk da bambancin jam’iyyun siyasa, wannan na nuna shugabanci nagari kenan, kuma jama’a ne a gabanshi.

“Sarkin ya bayyana goyon bayansa da kokarin da Gwamna Matawalle ke yi na samar da zaman lafiya a jahar Zamfara, kuma ya yi alkawarin cigaba da gudanar da addu’o’i domin samun nasararsa da nasarar shugaban kasa.” Inji shi.

Da yake nasa jawabi, Gwamna Matawalle ya gode ma Sarkin Daura daya nadashi wannan sarauta, kuma ya yi alkawarin cigaba da nuna dukkanin kyawawan halayen da suka yi sanadiyyar cancantarsa da samun wannan sarauta.

Daga karshe yace ba zai yi kasa a gwiwa wajen tabbatar da tsaro a jahar Zamfara ba, kuma zai cigaba da baiwa shugaban kasa dukkanin goyon bayan da yake bukata don kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng