Wata sabuwa: Za a fara koyar da harshen Fulatanci a makarantun Zamfara

Wata sabuwa: Za a fara koyar da harshen Fulatanci a makarantun Zamfara

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da shirinta na gabatar da harshen Fulatanci a jadawalin makarantun jihar.

An tattaro cewa Gwamnatin ta sanar da wannan yunkuri ne a yayinda take shirin fara gina rugage a jihar a cikin wannan makon.

Gwamnan jihar, Bello Matawalle ya bayyana shirin kaddamar da harshen ne a garin Gusau, babban birnin jihar a lokacin da ya karbi tsarin gina rugagen.

Matawalle ya ce "Tun da mun dauki alkawarin bude makarantun firamare da sakandire a sabbin rugagen da zamu gina, za mu tabbatar an yi amfani da harsunanmu na gargajiya don raya su."

Gwamnan ya bayyana cewa wannan zai bunkasa harsunan gargajiya musamman ga yara manyan gobe.

Tuni Gwamna Matawalle ya umarci ma'aikatar ilimin jihar ta gaggauta fara aiki kan sabon tsarin a makarantu.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Dakarun soji sun kashe yan ta’adda da dama a tafkin Chadi

Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin da suka rungumi tsarin kafa ruga tun bayan da gwamnatin tarayya ta bayyana aniyarta na kafa shirin, sannan kuma jihar ta zamo ta farko a jerin jihohi da ta fara aikin gina rugagen.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya, Dakta Supo Ayokunle, tare da wasu jiga-jigan kungiyar da kuma wasu manyan kungiyoyin addinin Kirista da suka hadar da babban limanin nan, Fasto Enoch Adeboye, sun nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya yi watsi da tsarin nan na gina wuraren kiwon dabbobi da aka fi sani da Ruga.

Wannan kira na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka gabatar yayin taron kungiyoyin kiristocin Najeriya da aka gudanar a Cocin Shepherd Hill Baptist da ke birnin Ikko na jihar Legas a ranar Asabar da ta gabata.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel