Jihar Zamfara
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, ya koka ga shugaban ƙasa Buhari da gwamnan Zamfara kan halin da yan Najeriya ke ciki a arewa musamman a Zamfara.
Mako biyu bayan da wasu 'yan bindiga dauke da makamai suka tare babban titin Kaduna zuwa Abuja tare da sace Sarkin Bungudu na jihar Zamfara,Alhaji Hassan Attah.
Miyagun 'yan bindiga sun kwashi kashin su a hannun sojoji da jami'an yan sanda, yayin da suka yi kokarin kai mugun hari garin Shinkafi, dake jihar Zamfara.
Ana ci gaba da fuskantar matsalolin sace-sace da kashe-kashen mutane a jihar Zamfara duk da cewa, gwamnati ta ba da umarnin katse hanyoyin sadarwa a jihar.
A wata fira da kafar watsa labarai ta BBC Hausa, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya yi tsokacin kan zancen ranar da za'a maida hanyoyin sadarwa a jihar.
A cewar majiyoyin, daruruwan mayakan, wadanda ake kyautata zaton ’yan kungiyar Ansaru ne sun rika shiga garuruwa a kan babura, kafin daga bisani su kafa tuta.
Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara, ya ce jiharsa ta canza shawararta kan tattaunawa da 'yan bindiga saboda yaudarar gwamnatinsa da suka yi, TheCable tace.
A halin yanzu ‘Yan bindigan da ke aikata ta’asa a jihar Zamfara suna ta tserewa sakamakon matakan tsaro da gwamnati ta dauka da kuma aikin soji da ke gudana.
Rahotanni ya nuna cewa kimanin dalibai 75 da aka sace daga Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Kaya, karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara sun samu 'yanci.
Jihar Zamfara
Samu kari