Bayan mako 2 da sace sarkin Bungudu, babu amo balle labarinsa

Bayan mako 2 da sace sarkin Bungudu, babu amo balle labarinsa

  • Bayan mako biyu da miyagun 'yan bindiga suka sace sarkin Bungudu, har yau babu amo balle labarinsa
  • An gano cewa 'yan bindigan sun karba miliyan 20 daga iyalan daya daga cikin wadanda aka sace tare da basaraken amma basu sako shi ba
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Jalige, ya tabbatar da cewa rundunar ta na iyakar kokarin ta wurin ganin ta ceto sarkin

Kaduna - Mako biyu bayan da wasu 'yan bindiga dauke da makamai suka tare babban titin Kaduna zuwa Abuja tare da sace Sarkin Bungudu na jihar Zamfara, Alhaji Hassan Attahiru da wasu matafiya, har yanzu shiru ake ji.

Daily Trust ta ruwaito yadda 'yan bindigan suka tare babban titin da tsakar ranar 14 ga watan Satumba kuma suka sace Sarkin da wasu matafiya.

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Bayan mako 2 da sace sarkin Bungudu, babu amo balle labarinsa
Bayan mako 2 da sace sarkin Bungudu, babu amo balle labarinsa. Hoto daga Daily Trust
Source: Facebook

Amma kuma, mako biyu bayan aukuwar mummunan lamarin, babu abinda aka ji game da basaraken.

Majiyar tsaro ta sanar da Daily Trust cewa 'yan bindiga sun bukaci kudin fansa har miliyan dari daga iyalan daya daga cikin wadanda aka sace bayan sun karba miliyan 20 daga 'yan uwansa kuma suka ki sakinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya ce jami'an tsaro suna iyakar kokarinsu wurin ganin sun ceto basaraken da sauran matafiyan da aka sace a ranar.

"Muna fatan ceto su ba tare da ko kwarzane ya same su ba duk da akwai abubuwa da yawa da muke yi ba tare da mun sanar da jama'a ba.
"Amma ina tabbatar muku muna aiki wurin ganin mun samo sarkin da sauran wadanda aka sace da ransu," yace.

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Osinbajo ya bayyana halin da yankunan kasar nan za su shiga idan Najeriya ta rabu

A wani labari na daban, Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce 'yan Najeriya ne za su wahala idan aka raba kasar nan. Ya sanar da hakan ne a ranar Litinin yayin da ya karba bakuncin shugabannin kungiyar 'yan jarida na kasa a fadar Aso Villa da ke Abuja.

Kamar yadda takardar da Laolu Akande, mai magana da yawun Osinbajo ya fitar, ya ce akwai bukatar a karfafa hadin kai a kasar nan kuma ya shawarci 'yan jarida da su kasance masu kwarewa yayin sauke nauyin da ke kansu.

"Najeriya kasar mu ce, mu 'yan jarida, 'yan siyasa ko kuma shugabannin addinai. Kasar mu ce kuma dole ne mu yi duk abinda ya dace wurin tabbatar da zaman lafiya tare da hadin kan kasar, hakan ya na da amfani," yace.

Read also

'Yan fashin daji da ISWAP a Sokoto: Sojin Najeriya sun yi rugu-rugu da 'yan ta'adda, Jami'ai

Source: Legit

Online view pixel