An bankado sabbin mafakar ‘yan bindigar Zamfara da ke tserewa

An bankado sabbin mafakar ‘yan bindigar Zamfara da ke tserewa

  • 'Yan bindigar da suka addabi al'umma a jihar Zamfara na ci gaba da tserewa tun bayan da gwamnati ta dauki matakan tsaro masu tsauri a kansu
  • Majiyoyi sun bayyana cewa a yanzu yan bindigar na tserewa yankunan Kebbe da Lambar Tureta a jihar Sokoto da kuma Birnin-Gwari a Kaduna
  • An tattaro cewa luguden wutan da dakarun soji ke yi kan yan ta'addan na haifar da 'ya'ya masu idanu

Zamfara‘Yan bindigan da ke aikata ta’asa a Zamfara a halin yanzu suna ta guduwa sakamakon matakan tsaro da gwamnati ta dauka da kuma aikin soji da ke gudana.

Don sanya su cikin damuwa, Gwamnatin Tarayya ta rufe hanyar sadarwar waya yayin da gwamnatin jihar ta rufe wasu kasuwannin da ke aiki a kowane mako.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare motar jigon PDP sun yi awon gaba da shi da direbansa

An bankado sabbin mafakar ‘yan bindigar Zamfara da ke tserewa
‘Yan bindigar Zamfara da ke tserewa suna komawa Sokoto da Kaduna Hoto: The Punch
Asali: UGC

Ko da yake an samu wasu koma-baya, da yawa sun ce aikin ya cimma nasara sosai.

Da yake tsokaci kan wannan, Gwamna Bello Matawalle ya ce yawan hare-haren da jami'an tsaro ke kaiwa 'yan fashi ya sa sun sake neman sulhu da gwamnati.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan, wanda ya yi watsi da zabin tattaunawa, ya ce wakilan 'yan fashi sun sanar da shi cewa sun tuba kuma suna son tattaunawa da gwamnati.

Ya lura cewa wasu daga cikin 'yan fashin suna tserewa daga Zamfara zuwa wasu jihohi sakamakon sabbin matakan tsaro da gwamnatin jihar ta bullo da su.

Jaridar Daily Trust ta kuma rahoto cewa ta gano wasu sabbin wuraren da ‘yan bindigar ke yada zango tun lokacin da aka fara yi masu ruwan bama-bamai.

Daga cikin wuraren da suka tsere, a cewar majiyoyi akwai:

Kara karanta wannan

Kebbi: Iyayen daliban FGC Yauri sun cire rai gwamnati za ta karbo musu 'ya'yansu

1. Kebbe a Sokoto

2. Lambar Tureta a Sokoto

3. Birnin-Gwari a Kaduna

Rekeb, wani sanannen ɗan fashi ya tabbatar wa jaridar Daily Trust da komawar wasu daga cikin yan bindigar, amma ya yi alfahari da cewa shi da sauran manyan masu ta’addanci suna ci gaba da kasancewa a cikin “sanannen wurin da suke a Zamfara”.

Yadda dakile layin wayoyin GSM ya jawo ‘Yan bindiga suka kai wa Sojoji hari a Zamfara

A wani labarin, mun ji cewa harin da aka kai wa dakarun jami’an tsaro a jihar Zamfara a ranar Asabar ya yiwu ne saboda kashe hanyoyin sadarwa da aka yi.

‘Yan bindiga sun shiga sansanin runduna da ke Mutumji, suka kashe sojojin ruwa tara, sojan kasa daya da wani jami’in ‘dan sanda, sannan suka saci makamai.

Rahoton yace abin da ya faru shi ne miyagun sun yi amfani da damar rashin sadarwa, suka kai harin.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

Asali: Legit.ng

Online view pixel