An cafke kasurgumin kwamandan 'yan bindigan da ya addabi jihar Zamfara

An cafke kasurgumin kwamandan 'yan bindigan da ya addabi jihar Zamfara

  • 'Yan sanda a jihar Zamfara sun kame wani kasurgumin dan bindigan da ya addabi jihar Zamfara
  • An kuma kame wasu 'yan bindiga sama da 21 tare da shahararren kwamandan nasu da aka kame
  • A halin yanzu, 'yan sanda sun bayyana cewa, suna kan bincike kan ayyukan 'yan bindigan

Zamfara - Ayuba Elkanah, kwamishinan 'yan sanda a Zamfara, ya ce rundunar 'yan sanda ta cafke wani kasurgumin kwamandan 'yan bindiga mai suna Bello Rugga, The Cable ta ruwaito.

Elkanah ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da yake gabatar da wanda ake zargi kwamanda ne tare da wasu mutane 21 da ake zargi da fashi da makami a Gusau.

Ya ce an kashe wasu 'yan bindiga biyar yayin wani samame da suka kai a karamar hukumar Gummi ta jihar.

Read also

Sanatan APC ya maida wa Sanusi martani kan ikirarin cewa tattalin Najeriya ya kusa ya ruguje

An cafke kasurgumin kwamandan 'yan bindigan da ya addabi jihar Zamfara
'Yan sandan Najeriya | Hoto: dailynigerian.com
Source: UGC

Sanarwar ta ce:

"A ranar 1 ga Oktoba, 2021, 'yan sanda masu dabarun yaki da 'yan ta'adda a kewayen Gummi, sun yi aiki da rahoton bayanan sirri, sun kai hari Gidan Bita, Malanjara da dajin Kagara, suka kama wani kasurgumin kwamandan 'yan bindiga, Bello Rugga."
“Wanda ake zargin ya kasance kwamanda ga wani shugaban yan ta’addan da ake nema, wanda aka fi sani da Turji.
“Rugga shine ke kula da Gummi, Gidan Bita, Malanjara da Kagara da ke karamar hukumar Gummi ta jihar.
"Ya shirya jerin hare-hare a yankin wanda ya kai ga kisan gilla ga mutanen da ba su ji ba ba su gani ba tare da yin garkuwa da wasu da yawa don neman kudin fansa."

Elkannah ya ce wanda ake zargin yana da 'yan bindiga da yawa a karkashinsa a lokacin da aka kama shi, ya kara da cewa an kwato bindigogi kirar AK-47 daga hannunsa.

Read also

Yan sanda sun kame waɗanda ake zargi da kisan babban malamin Addini a jihar Kano

A cewarsa, wanda ake zargin a halin yanzu yana hannun 'yan sanda kuma ana gudanar da bincike.

Ya ce an kuma kama wasu mutum biyu da ake zargi da hada baki da ‘yan bindiga yayin da suke kai manyan kayayyaki na miyagun kwayoyi, buhunan tabar wiwi, da man fetur zuwa sansanin 'yan bindigan.

Ya ce 'yan bindigar da aka kashe a yayin farmakin su ne ke kai hare-hare da dama a sassa daban-daban na jihar, musamman ma yankin sanatan Zamfara ta Yamma.

'Yan sanda sun cafke tsageru 13 da ake zargi 'yan bindiga ne kuma barayin shanu a Katsina

Rundunar ‘yan sanda a jihar atsina ta cafke mutane 13 da ake zargi da hannu a fashi da makami, satar shanu, garkuwa da mutane da safarar makamai da kuma ta’addancin kan 'yan jihar da ba su ji ba su gani ba.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar Katsina, Gambo Isah ne ya bayyana hakan, Daily Nigerian ta ruwaito.

Read also

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 2 su na tsaka da amsar kuɗin fansa

Mista Isah ya ce kamun wadanda ake zargin ya kasance wani bangare na nasarorin da rundunar 'yan sandan jihar ta samu a baya-bayan nan a ci gaba da yaki da miyagun laifuka da aikata laifuka a jihar.

A cewarsa:

"‘Yan sanda a Katsina sun samu nasarar cafke wani matashi dan shekara 30 da ake kira DAN OGA, na kauyen Sabaru, karamar hukumar Tsafe, Jihar Zamfara, wani sanannen dan bindiga.
“A lokacin da ake gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa yana karkashin ikon wani mai suna Chairman, wani sanannen dan bindiga da ke boye a cikin dajin Zamfara.
”Ya furta cewa yana da hannu a harin da aka kai kauyen Unguwar Dodo, na karamar hukumar Tsafe ta Zamfara inda aka fasa shaguna aka sace kayan abinci da sauran kayayyaki.
“Wanda ake zargin ya kuma ambaci Hakimin unguwarsu da sauran mutane a cikin wadanda suke tare da shi."

Read also

'Yan fashi sun afka wa coci domin sace kudi, sun daba wa mai gadi wuka a Abuja

Rahoto: Halin da ake ciki na harin 'yan bindiga duk da katse hanyoyin sadarwa a Zamfara

A wani labarin, alamu sun bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da samun kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar Zamfara duk da katse hanyoyin sadarwa a jihar.

Yayin da katsewar da kokarin sojoji ya rage barnar 'yan bindiga tare da kashe su, wasu mazauna jihar sun shaida wa BBC Hausa cewa an ci gaba da kai hare-hare da sace-sacen a jihar.

Don haka, duk da rokon da suke yi wa gwamnatin jihar na tsagaita wuta, kamar yadda Gwamna Bello Matawalle ya bayyana a ranar 10 ga Satumba, 'yan bindigan sun ci gaba da kai hari kan mazauna jihar.

Source: Legit.ng

Online view pixel