‘Yan sanda sun kama kwamandan ‘yan bindiga, an hana amfani da bakin gilashin mota a Zamfara

‘Yan sanda sun kama kwamandan ‘yan bindiga, an hana amfani da bakin gilashin mota a Zamfara

  • ‘Yan sanda a jihar Zamfara sun kama wani shahararren kwamandan ‘yan fashi wanda aka fi sani da Bello Ruga
  • Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba Elkana, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai ya ce an cafke Bello a sansanin ‘yan fashi da ke karamar hukumar Gummi ta jihar
  • Har ila yau an hana amfani da bakin gilashin mota a jihar

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce ta cafke daya daga cikin fitattun kwamandojin ‘yan fashi, Bello Ruga.

Channels TV ta ruwaito cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Ayuba Elkana, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai ya ce an cafke Bello, wanda aka fi sani da Bello Dan Malankara, a sansanin ‘yan fashi da ke karamar hukumar Gummi ta jihar.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kame waɗanda ake zargi da kisan babban malamin Addini a jihar Kano

‘Yan sanda sun kama kwamandan ‘yan bindiga, an hana amfani da bakin gilashin mota a Zamfara
‘Yan sanda sun kama kwamandan ‘yan bindiga, an hana amfani da bakin gilashin mota a Zamfara Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya ce:

"A ranar 1 ga watan Oktoba 2021, 'yan sanda da ke yaki da 'yan ta'adda a kewayen Gummi sun yi aiki da rahoton sirri kuma sun kai hari Gidan Bita, Malankare, da dajin Kagara don neman wani sanannen dan fashi da ake kira Bello Rugga.
“Dan ta’addan wanda ya kasance daya daga cikin kwamandojin Turji shi ne ke kula da Gummi, Gidan Bita, Malankare, da Kagara da ke karamar hukumar Gummi.
“Ya kasance mai ba da umarni a jerin hare-hare da garkuwa da mutane a Gummi wanda ya haifar da kisan gilla ga mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, da kuma sace mutane da yawa inda aka biya fansa. Wanda ake zargin yana da 'yan fashi da yawa a karkashinsa kuma yana da bindigogin AK 47.”

Kara karanta wannan

Kano: Matashi mai shekaru 21 ya jagoranci fashi a gidan maƙwabcinsa

A halin da ake ciki, Elkana ya ba da sanarwar cewa a gaggauta cire duk motocin da ke da bakin gilashi ba tare da izini ba.

Ya kuma umarci 'yan sanda da su kama tare da gurfanar da masu ababen hawa da basu da lamba ba a kan dukkan hanyoyin jihar.

Har ila yau rahoton ya ce Kwamishinan ‘yan sandan ya kuma yi karin haske kan matsayin matakan da gwamnatin jihar ta sanar na duba ayyukan ‘yan bindiga a Zamfara.

A cewarsa, dokar hana daukar fasinja sama da daya a kan babur, da kuma amfani da babura masu makama a kananan hukumomi 13 da wasu sassan Gusau, na nan daram.

Elkana ya gargadi mazauna garin kan rashin bin dokar rufe kasuwannin mako-mako a jihar, baya ga Gusau.

Ya tunatar da su game da takaita zirga -zirgar shige da fice daga kananan hukumomi 13 daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma, sannan daga karfe 8 na yamma zuwa 6 na safe a babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 2 su na tsaka da amsar kuɗin fansa

Kwamishinan ‘yan sandan, ya bayyana cewa an tsawaita zirga -zirga a cikin garin Gusau zuwa karfe 12 na safe, kamar yadda Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Ibrahim Dosara ya sanar.

Elkana ya roki mazauna yankin da su kara hakuri tare da marawa gwamnati baya a kokarin ta na dawo da zaman lafiya da tsaro a jihar.

Gwamna Matawalle ya yi umarnin dawo da layukan sadarwa a Gusau

A wani labarin, Gwamna Bello Mohammed Matawalle na Zamfara ya ba da umarnin dawo da layukan sadarwar tarho a Gusau, babban birnin jihar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Tun daga watan Satumbar da ya gabata ne aka datse layukan sadarwa a cikin jihar a matsayin wani yunkuri na matakan magance fashi da makami.

A cikin wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman kan wayar da kan jama'a, kafofin watsa labarai da sadarwa, Zailani Bappa, umarnin ya fara aiki a yau Juma’a, 1 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

'Yan fashi sun afka wa coci domin sace kudi, sun daba wa mai gadi wuka a Abuja

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

iiq_pixel