Sojoji da Jiragen Yaki Sun Zafafa Hare Hare, Sun Rutsa Yan Bindiga Ta Sama da Kasa a Jihohi 2
- Dakarun Sojoji Najeriya sun kara zafafa ayyukan yaki da ‘yan ta’adda da kungiyoyi masu dauke da makamai a Katsina da Zamfara
- Rundunar sojin ta ce an kai samame ta kasa da sama kan yan bindiga a maboyarsu a karkashin Operation CLEAN SWEEP IV
- Rahoto ya ce hare-haren sun tarwatsa sansanonin ‘yan ta’adda tare da kashe wasu daga cikinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Rundunar sojin Najeriya ta kara zafafa kai hare-hare yaki kan ‘yan ta’adda da kungiyoyi masu dauke da makamai a jihohin Katsina da Zamfara.
Dakarun sun kai hare-hare ta sama da kasa kan yan bindiga a wadannan jihohi a karkashin Operation CLEAN SWEEP IV, wani sabon mataki na Operation Fansan Yamma.

Source: Facebook
Rahoton Punch ya kawo cewa rundunar hadin gwiwar Operation FANSAN YAMMA ta ce an tsara aikin ne domin tarwatsa hanyoyin sadarwa da ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda da rage karfinsu a yankin Arewa maso Yamma.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da jami’in yada labarai na Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar ranar Alhamis.
Ya ce Operation CLEAN SWEEP IV ya kunshi ayyukan soji na kasa da kuma na sama da ake gudanarwa lokaci guda kan barazanar da aka gano a yankin.
Sojoji sun kai samame Katsina
Aliyu Danja ya ce an riga an kara yawan ayyukan soji a sassan yankin tun bayan fara Operation CLEAN SWEEP IV.
A Jihar Katsina, sojojin Sector 2 sun gudanar da samamen share fagen yaki a ranar 12 ga Agusta a wasu wuraren da ake zargin ‘yan ta’adda na fakewa a Karamar Hukumar Dutsinma.
Ya ce samamen ya kara matsin lamba kan ‘yan ta’addan, lamarin da ya tilasta musu barin wuraren da suke tare da guduwa zuwa dazuzzukan da ke kusa.
An kai hare-haren sama Zamfara
A Jihar Zamfara kuma, rundunar Operation Fansan Yamma ta kai hare-haren sama kan ‘yan ta’adda bayan samun bayanan sirri kan yadda wasu miyagu da ke kan babura suka taru a Karamar Hukumar Anka.
Aliyu Danja ya ce hare-haren sama sun kashe wasu daga cikin ‘yan ta’addan, yayin da wadanda suka tsira suka bar baburansu suka tsere zuwa dazuzzukan da ke kewaye.
Ya ce:
“Daga nan, dakarun sojojin sama sun gano sauran ‘yan ta’addan tare da kai musu hari.”

Source: Twitter
Rundunar ta ce daya daga cikin muhimman manufofin Operation CLEAN SWEEP IV shi ne dakile tare da wargaza kungiyar ta’addancin Lakurawa a fadin Arewa maso Yamma.
Sojojin Najeriya sun ceto mutane a Kogi
Kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta jagoranci wani samame da ya kai ga ceto mutane 16 da aka yi garkuwa da su a jihar Kogi.
An gudanar da aikin ceto ne bayan da jami'an tsaro suka samu bayanan sirri kan inda aka kai mutanen da aka sace.
An sace mutanen ne ranar Lahadi, 9 ga Agusta 2026, lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai hari kan matafiya a hanyoyin Ojuwo–Ajengo–Memarebo da Ojiwo–Itobe.
Asali: Legit.ng

