Dokar Zabe Ta Tanadi Tarar Naira Miliyan 50 kan Yin Kamfen Bisa Addini

Dokar Zabe Ta Tanadi Tarar Naira Miliyan 50 kan Yin Kamfen Bisa Addini

  • Jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar da suka gudanar da yaƙin neman zaɓe bisa addini ko ƙabilanci na iya fuskantar tarar da ta kai Naira miliyan 50
  • Dokar ta tanadi hukunci ga ɗan takarar da ya karya ta, yayin da kafafen yaɗa labarai da suka karya ƙa’idojin kamfen za su iya fuskantar tarar da ta kai N5m
  • A ƙarƙashin ƙa’idojin, jam’iyyu da ‘yan takararsu za su fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya daga gobe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Dokar Zaɓe ta 2026 ta tanadi hukunci mai tsauri kan jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar da suka yi amfani da addini ko ƙabilanci wajen neman kuri’un jama’a gabanin babban zaɓen shekara mai zuwa.

Sashe na 99 da na 101 na dokar sun tanadi matakai daban-daban na hukunci ga jam’iyyu, ‘yan takara da kafafen yaɗa labarai da suka karya ƙa’idojin yaƙin neman zaɓe.

Kara karanta wannan

Shugaban APC zai hada mutum miliyan 1 su zabi Tinubu a Ondo a 2027

Shugaban hukumar zabe ta kasa
Shugaban INEC, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Tarar N50m kan jam’iyyun siyasa

The Nation ta rahoto cewa sashe na 101 na dokar zaɓe ta 2026 ya haramta gudanar da yaƙin neman zaɓe bisa tushen addini, inda ya tanadi tarar da ta kai Naira miliyan 50 ga jam’iyyar siyasar da ta karya wannan tanadi.

Ɗan takarar da aka samu da laifin yin yaƙin neman zaɓe bisa addini ko ƙabilanci kuma zai iya fuskantar tarar da ta kai Naira miliyan 3.

Matakin ya zo ne yayin da ake shirin fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa a Najeriya.

Batun ƙa’idojin kamfen

Sashe na 99 na Dokar Zaɓe ta 2026 ya tanadi tsarin gudanar da yaƙin neman zaɓe, tare da hukunta masu karya ƙa’idojin da tarar da ta kai Naira miliyan 5.

Sashe na 99(1) ya bayyana cewa dole ne ɗan takara da jam’iyyarsa su gudanar da yaƙin neman zaɓe bisa ƙa’idoji da dokokin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta tsara.

Kara karanta wannan

Bayan turmusa ta a zaɓen Osun, APC ta faɗi matakin da za ta ɗauka nan gaba

Wajen da aka yi zaben Osun
Jami'an INEC a wajen gudanar da zaben Osun. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Sashe na 99(2) kuma ya hana amfani da kayan aikin gwamnati, ciki har da kafafen yaɗa labarai, wajen fifita ko cutar da wata jam’iyya ko ɗan takara a zaɓe.

Dokar ta kuma buƙaci a bai wa jam’iyyu da ‘yan takara damar samun lokacin yaɗa manufofinsu daidai a kafafen yaɗa labarai na gwamnati.

Batun addini a zaɓen Osun

A wani labarin, mun ruwaito cewa Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulmi (MURIC) ta zargi Hukumar INEC da tauye haƙƙin wasu mata Musulmi da suka sanya hijabi yayin zaɓen gwamnan Jihar Osun da aka gudanar.

Kungiyar MURIC ta yi zargin cewa an hana dubban mata Musulmi yin zaɓe saboda hijabin da suke sanye da shi a lokacin zaben Osun.

Ƙungiyar, a cikin wata sanarwa da shugaban ta, Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar, ta ce lamarin ya faru a wurare da dama a jihar, tana mai cewa hakan ya jefa matan cikin tilastawa, wulakanci da kuma tauye musu haƙƙin zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng