Miyagun yan bindiga da dama sun sheka lahira yayin da yan sanda da Sojoji suka dakile hari a Zamfara
- Rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara ta bayyana ainihin abinda ya faru a garin Shinkafi na jihar Zamfara
- A wata sanarwa da kakakin yan sandan jihar, Muhammed Salihu, ya fitar, yace sojoji da yan sanda sun sheke yan bindiga da yawa
- A cewarsa, maharan sun yi ƙoƙarin kai hari garin Shinkafi, amma jami'an tsaro suka fatattake su
Zamfara - Rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara ta yi ikirarin cewa yan bindiga da dama sun mutu yayin da suka yi kokarin kai hari garin Shinkafi, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Rundunar ta faɗi haka ne yayin da take martani kan rahoton dake yawo cewa an farmaki garin Shinkafi da caji ofis ranar Lahadi.
A wata sanarwa da kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara, Mohammed Shehu, ya fitar, yace haɗin guiwar jami'an yan sanda da sojiji sun daƙile harin.
'Yan Bindiga Sun Kai Hari Shinkafi Bayan Tura Wasiƙa, Sun Kutsa Ofisoshin 'Yan Sanda Sun Saci Bindigu
Shin dagaske yan bindiga sun kai hari caji ofis?
Wani sashin sanarwar yace:
"Babu wani hari da aka kai caji ofis ɗin yan sanda dake ƙaramar hukumar Shinkafi ko wani yanki a jihar Zamafara, kamar yadda wasu ke yaɗawa."
"Hakanan kuma rahoton kai hari garin Shinkafi ba gaskiya bane. Abinda ya faru shine, ranar 24 ga watan Satumba, yan bindiga sun yi nufin kai hari garin Shinkafi."
"Amma rundunar yan sanda da kuma haɗin guiwar jami'an sojoji dake zaune a yankin sun samu nasarar dakile harin, tare da hallaka maharan da dama."
Shin an kashe wasu daga cikin jami'an tsaro?
Sanarwan ta cigaba da cewa maharan ba su kashe ko mutum ɗaya daga cikin jami'an tsaron ba, basu samu nasarar sace kowa ba.
Punch ta rahoto sanarwar na cewa:
"A halin yanzu komai ya koma dai-dai a yankin, yayin da jami'an tsaro suka ɗauki matakan da ya dace cikin gaggawa."
A wani labarin na daban kuma Jam'iyyar Hamayya PDP ta lallasa APC mai mulki a zaɓen karamar hukumar Kajuru
Jam'iyyar hamayya PDP ta lashe zaɓen kujerar ciyaman na ƙaramar hukumar Kajuru dake jihar Kaduna.
Hakanan kuma, PDP ta lashe kujerun kansiloli guda 9, yayin jam'iyyar APC mai mulki ta lashe kujerar kansila ɗaya tal.
Asali: Legit.ng