Da dumi-dumi: Gwamna Matawalle ya yi umarnin dawo da layukan sadarwa a Gusau

Da dumi-dumi: Gwamna Matawalle ya yi umarnin dawo da layukan sadarwa a Gusau

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta ba da umarnin dawo da layukan sadarwa a fadin babban birnin Gusau
  • Mai ba gwamnan shawara na musamman a kafofin watsa labarai da sadarwa, Zailani Bappa, ya ce umarnin ya fara aiki a yau Juma’a, 1 ga watan Oktoba
  • Ya ce an yanke wannan shawarar ne domin rage wahalhalun da bangarorin gwamnati da masu zaman kansu ke fuskanta a jihar

Gusau, jihar Zamfara - Gwamna Bello Mohammed Matawalle na Zamfara ya ba da umarnin dawo da layukan sadarwar tarho a Gusau, babban birnin jihar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Tun daga watan Satumbar da ya gabata ne aka datse layukan sadarwa a cikin jihar a matsayin wani yunkuri na matakan magance fashi da makami.

Read also

Telegram ta yi fintinkau yayin da Facebook, WhatsApp da Instagram suka daina aiki

Da dumi-dumi: Gwamna Matawalle ya yi umarnin dawo da hanyoyin sadarwa a Gusau
Gwamna Matawalle ya yi umarnin dawo da hanyoyin sadarwa a Gusau Hoto: thecable.ng
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman kan wayar da kan jama'a, kafofin watsa labarai da sadarwa, Zailani Bappa, umarnin ya fara aiki a yau Juma’a, 1 ga watan Oktoba.

Bappa ya bayyana cewa maido da cibiyar sadarwa a babban birnin jihar ya zama wajibi bayan nasarar da aka samu a yaki da 'yan fashi.

Ya kara da cewa an yanke wannan shawarar ne domin rage wahalhalun da bangarorin gwamnati da masu zaman kansu ke fuskanta a jihar, Channels TV ta ruwaito.

Ya ce:

"Gwamnan ya ba da umurnin dawo da sabis din wayoyi a cikin babban birnin jihar Gusau kadai daga yau Juma'a, 1 ga Oktoba, 2021."
“Maido da sabis din a Babban Birnin Jihar yana da mahimmanci bayan gagarumar nasarar da aka samu a yakin da ake yi da masu fashi da makami a jihar da kuma rage wahalhalun da bangarori masu zaman kansu da na gwamnati ke fuskanta.

Read also

Labarin gimbiyar da ta bar masarautarsu ta auri talaka ya dauki hankalin jama'a

“Gwamnati ta ga ya zama dole ta sauƙaƙa matakan bayan nasarar da aka samu wanda babu shakka ya tarwatsa ƙungiyar masu aikata laifuka da ta addabi jihar wanda ya haifar da nasarorin da jami’an tsaro suka samu a kansu.
"Gwamna Matawalle ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da sanya ido kan abubuwan da ke faruwa kuma za ta sanar da ƙarin shawarwari da Gwamnati ta yanke kan matakan da aka ɗauka daidai."

Bayan katse hanyoyin sadarwa, mun damƙe masu kaiwa yan bingida bayanai 2,000 a Zamfara, Kwamishina

A baya mun kawo cewa sama da yan leken asirin yan bindiga 2,000 aka cafke a jihar Zamfara sanadiyyar datse hanyoyin sadarwa a jihar, a cewar kwamishinan yaɗa labarai, Alhaji Ibrahin Dosara.

Kwamishinan ya bayyana haka ne a jihar Kaduna, yayin da yake jawabi game da Operation ɗin sojoji a jihar Zamfara, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Read also

An yi jana'izar mahaifin kakakin majalisar Zamfara da ya rasu a hannun 'yan bindiga

Yace an tsananta bincike kan waɗanda ake zargi da leken asirin domin su faɗi masu ɗaukar nauyinsu da kuma abokan aikinsu.

Source: Legit.ng

Online view pixel