Rahoto: Halin da ake ciki na harin 'yan bindiga duk da katse hanyoyin sadarwa a Zamfara

Rahoto: Halin da ake ciki na harin 'yan bindiga duk da katse hanyoyin sadarwa a Zamfara

Alamu na nuna an tsawaita umarnin katse hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara. Rahoto ya bayyana yadda mazauna ke fuskantar barazanar tsaro duk da katse hanyoyin sadarwa da aka yi a cikin jihar

Alamu sun bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da samun kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar Zamfara duk da katse hanyoyin sadarwa a jihar.

Yayin da katsewar da kokarin sojoji ya rage barnar 'yan bindiga tare da kashe su, wasu mazauna jihar sun shaida wa BBC Hausa cewa an ci gaba da kai hare-hare da sace-sacen a jihar.

Don haka, duk da rokon da suke yi wa gwamnatin jihar na tsagaita wuta, kamar yadda Gwamna Bello Matawalle ya bayyana a ranar 10 ga Satumba, 'yan bindigan sun ci gaba da kai hari kan mazauna jihar.

Kara karanta wannan

An kama ma’aurata kan kashe dansu tare da binne shi cikin sirri saboda ‘rashin ji’

Rahoto: Halin da ake ciki na harin 'yan bindiga duk da katse hanyoyin sadarwa a Zamfara
'Yan bindiga | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Duk da haka, alkaluman da aka samu daga Hukumar Kula da Tsaro ta Najeriya, wani shiri na Majalisa kan Harkokin Kasashen Waje wanda tsohon jakadan Amurka a Najeriya, John Campbell ya gyara, ya nuna cewa ana ci gaba da yin garkuwa da mutane da kashe-kashe a Zamfara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ranar 3 ga watan Satumba, ranar da katsewar sadarwa ta fara aiki a Zamfara, an ce mutane hudu sun mutu yayin da aka sace wasu kimanin 50 lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai hari a gundumar Ruwan Dorawa da ke karamar hukumar Maru ta jihar.

A bangaren ci gaba, bayan kwana uku, an ba da rahoton cewa sojoji sun kashe 'yan bindiga 20 a wani hari ta sama a Shinkafi.

'Yan bindiga sun kuma kashe mutane hudu a Bugundu ta jihar Zamfara bayan sun kai hari ofishin 'yan sanda.

Kara karanta wannan

'Yan fashin daji ne ke kewaye da mu, Al'ummar Kaduna sun koka

A ranar 11 ga watan Satumba, yan bindiga sun kashe sojoji 12 a Mutumji, karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara. Sun kuma kashe fararen hula bakwai a kananan hukumomin Shinkafi da Zurmi a ranar 16 ga Satumba, inda suka kona gidan Kakakin Majalisar Jihar, Nasiru Magarya, a garin Magarya.

An tsawaita katse hanyoyin sadarwar na makonni biyu zuwa wani lokaci

Ana cikin irin wannan yanayin, da alama an tsawaita umarnin katse dukkan hanyoyin sadarwa a jihar, kamar yadda hukumar sadarwa ta Najeriya ta umarta.

Wannan kenan a saboda duk wani kokarin da aka yi don samun yawancin mazauna jihar ya ci tura yayin da mazauna yankin ba sa iya kira kuma ba a iya samunsu, duk da cewa katsewar za ta kasance na makwanni biyu “a matakin farko”.

Ya zuwa yammacin ranar Asabar, 25 ga watan Satumba, kiraye-kiraye da dama da wakilinmu ya yi ga mutane daban-daban a jihar basu shiga ba, wanda hakan ya nuna cewa ba a dage dokar katsewar ba a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun afkawa coci ana cikin ibada, sun kashe mutum 1, sun sace 3

Wani mazauni mai suna Shuaibu ya kuma ce a cikin wata hira cewa sukan yi tattaki zuwa jihar Sakkwato don yin waya saboda sun kasa yin hakan a kwaryar jihar su.

Sojin Najeriya sun kera motocin da kan iya hango 'yan ta'adda daga nisan tazara

A wani labarin, Babban hafsan sojojin kasa (COAS), Laftanar Janar Farouk Yahaya, a ranar Litinin 13 ga watan Satumba, ya ba da sabbin motocin sadarwa na tauraron dan adam wadanda za a tura su ga rundunoni daban-daban na soji a fadin kasar.

Motocin na dauke da kyamarori da kayan aikin lantarki na zamani, kuma rundunar sojan Najeriya ta Cyber ​​Warfare Command, Abuja ta kirkiresu, The Sun ta ruwaito.

Da yake jagorantar COAS yayin ziyarar duba motocin, Kwamandan, Cyber ​​Warfare Command, Birgediya Janar Adamu, ya ce motocin na hango abu daga nisan kilomita 6.5 kuma an sanya masu na'urorin da za su taimaka a hango abubuwa ko da cikin dare ne.

Kara karanta wannan

Gwamna Matawalle ya sanar da dalilin da yasa suka daina sasanci da 'yan bindiga

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.