Gwarazan yan sanda sun ceto iyalan kakakin majalisa da wasu mutum 11 daga hannun miyagu
- Jami'an yan sanda a jihar Zamfara, sun samu nasarar kubutar da mutum 5 daga cikin iyalan kakakin majalisar dokokin jihar
- Kwamishinan yan sanda, Ayuba Elkanah, yace jami'ai sun ceto wasu mutum 11 da mahara suka sace a Kauran Namoda
- Yace hukumar yan sanda na cigaba ƙoƙarin ceto mahaifin kakakin majalisar daga hannun miyagun da suka yi garkuwa da shi
Zamfara - Rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara, ranar Asabar, ta sanar da ceto iyalan kakakin majalisar dokokin Zamfara da aka sace tun 5 ga watan Agusta, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Kwamishinan yan sandan jihar, Ayuba Elkanah, shine ya tabbatar da haka yayin da ya gabatar da waɗanda aka ceto gaban manema labarai a Gusau.
Elkanah yace jami'ai sun ceto mutum 16, cikin su harda jaririya yar wata uku, Khaɗija Muazu, da mahaifiyarta, Hauwa Muazu.
Yace an samu nasarar ceto mutanen ne yayin da maharan suka tsere daga ruwan wutan sojoji, suka bar su a cikin dazuka.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mutun nawa ne iyalan kakakin majalisa da aka ceto?
Legit.ng ta tattaro cewa a kwanakin baya wasu miyagu sun yi awon gaba da mahaifin kakakin majalisar Zamfara, tare da mutum 5 daga cikin iyalansa a ranar 5 ga watan Agusta a Magarya, ƙaramar hukumar Zurmi.
Kwamishinan yan sandan yace an ceto mambobin iyalan kakakin ne a ranar 29 ga watan Satumba.
Waɗanda aka ceto ɗin sun haɗa da; Dahiru Sarki Magarya, Huwau Mu’azu Magarya, baby Khadija, Usman Magarya da Okasha Abdullahi Magarya.
Yan sanda sun ceto wasu mutum 11
Elkanah ya ƙara da cewa sauran mutum 11 da aka ceto, cikinsu harda mata huɗu, sun shiga hannun miyagun ne a Ƙauyen Magamin Tundu, ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda.
Yace a halin yanzun an gudanar da binciken lafiya ga waɗanda aka ceto kuma bada jimawa ba za'a haɗa su da iyalansu.
Kwamshinan ya tabbatar da cewa jami'an yan sanda na cigaba da kokarin ceto mahaifin kakakin majalisa, Alhaji Muazu Magarya, daga hannun yan bindiga.
A wani labarin kuma Sojoji sun hallaka yan fashi 394, yan ta'adda 85 a cikin mako uku, DHQ
Hedkwatar tsaro ta bayyana irin nasarorin da rundunar sojin Najeriya ta samu a faɗin kasa cikin makonni uku da suka shuɗe.
Hedkwatar tace dakarun soji sun hallaka yan fashi 394, da yan ta'adda 85 a hare-hare daban-daban ta sama da ƙasa da suka kaddamar.
Asali: Legit.ng