Mahaifin kakakin majalisa da malamin jami'a sun mutu a hannun 'yan bindiga
- Rahotanni sun bayyana cewa, mahaifin kakakin majalisar jihar Zamfara ya mutu a hannun 'yan bindiga
- Hakazalika, wani malamin jami'a daga jihar Kogi shi ma ya rasa ransa yayin da 'yan bindigan ke kokarin gudu
- A halin da ake ciki, 'yan sanda na aikin ceto sauran mutane 16 da aka sace daga cikin iyalan kakakin majalisar
Zamfara - Alhaji Muazu Abubakar, mahaifin kakakin majalisar jihar Zamfara, Nasiru Muazu Magarya, ya rasu sakamakon bugun zuciya yayin da yake tsare a mafakar 'yan bindiga.
Babban dan uwan marigayin, Malam Dahiru Saraki Magarya ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a ranar Asabar, kamar yadda jaridar Blueprint ta ruwaito.
An yi garkuwa da marigayin ne makonni takwas da suka gabata tare da matarsa, jariri dan makonni uku, Malam Magarya da wasu mutum biyu.
Malamin jami'a ya mutu a hannun 'yan bindiga
Hakazalika, wani tsohon ma'aikacin Kwalejin Ilimi ta Jihar Kogi (Fasaha) da ke Kabba, Julius Oshadumo, wanda 'yan bindiga suka yi garkuwa da shi a makwanni biyu da suka gabata, ya mutu a rikicin da ya barke tsakanin masu garkuwar da jami'an tsaron yankin yayin aikin ceto.
An yi garkuwa da da Julius ne ranar Lahadi biyu da suka gabata lokacin da wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka kai hari kan cocin ECWA da ke yankin Okedayo a Kabba, Jihar Kogi, inda aka kashe mutum daya sannan aka harbe-harbe kan wasu masu ibada.
Malam Magarya ya shaida cewa kasurgumin shugaban 'yan bindiga daya da aka fi sani da Kachalla ne ya sanar da shi kwana daya kafin kubutar da su cewa dan uwansa ya rasu ne sakamakon bugun zuciya.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba Elkanah, ya gabatar da wadanda aka ceto a gaban manema labarai a Gusau ranar Asabar 2 ga watan Oktoba.
Ya ce duk wadanda abin ya rutsa da su an duba lafiyarsu kuma za a mika su ga iyalansu, inji rahoton Daily Trust.
Ya ce wadanda abin ya rutsa dasu 16, ciki har da jariri dan wata uku, Khadija Muazu, da mahaifiyarta Hauwau Muazu, an kubutar da su kuma an dawo da su lafiya lokacin da 'yan bindigan suka tsere suka bar su a sansaninsu.
Elkanah, duk da haka, ya ba da tabbacin cewa ana kokarin ceto mahaifin kakakin daga wadanda suka yi garkuwa da shi.
'Yan sanda sun cafke tsageru 13 da ake zargi 'yan bindiga ne kuma barayin shanu a Katsina
A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda a jihar atsina ta cafke mutane 13 da ake zargi da hannu a fashi da makami, satar shanu, garkuwa da mutane da safarar makamai da kuma ta’addancin kan 'yan jihar da ba su ji ba su gani ba.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar Katsina, Gambo Isah ne ya bayyana hakan, Daily Nigerian ta ruwaito.
Mista Isah ya ce kamun wadanda ake zargin ya kasance wani bangare na nasarorin da rundunar 'yan sandan jihar ta samu a baya-bayan nan a ci gaba da yaki da miyagun laifuka da aikata laifuka a jihar.
Asali: Legit.ng