Ba Ranar Maida Sabis Na Sadarwa a Jihar Zamfara, Gwamna Matawalle Ya Yi Jawabi

Ba Ranar Maida Sabis Na Sadarwa a Jihar Zamfara, Gwamna Matawalle Ya Yi Jawabi

  • Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya bayyana cewa babu ranar maida hanyoyin sadarwa a jiharsa
  • Matawalle yace gwamnatinsa zata cigaba da tattaunawa da hukumomin tsaro lokaci bayan lokaci domin jin halin da ake ciki
  • Gwamnatin Katsina ta datse hanyoyin sadarwa a kananan hukumi 13 daga cikin 34 dake faɗin jihar

Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, yace datse sabis ɗin sadarwa a jihar zai cigaba da kasancewa har zuwa lokacin da jami'an tsaro suka ci galaba kan matsalar tsaro.

Hukumar sadarwa (NCC) ta umarci kamfanonin sadarwa su datse hanyoyin sadarwa a Zamfara na tsawon mako biyu a wani mataki na daƙile ayyukan yan bindiga a jihar.

Premium times ta rahoto yadda mutanen Zamfara suke tafiya zuwa jihar Sokoto da Fintua a jihar Katsina domin kiran waya, tura sakon karta kwana da kuma harkokin kuɗi.

Kara karanta wannan

SERAP Ta Aike da Budaddiyar Wasika Ga Shugaba Buhari Kan Datse Hanyoyin Sadarwa a Zamfara da Katsina

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle
Ba Ranar Maida Sabis Na Sadarwa a Jihar Zamfara, Gwamna Matawalle Ya Yi Jawabi Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Hana amfani da hanyoyin sadarwa zai ƙare ne a ranar Jumu'a, amma da yake hira da gidan Radio na BBC Hausa, Matawalle yace babu ranar maida sabis.

Yaushe za'a maida sabis a Zamfara?

Gwamnan yace:

"Ya zama wajibi mu cigaba da hakuri da rashin sadarwa, saboda babban fatan mu shine zaman lafiya ya dawo kuma mutane su tsira."
"Zamu cigaba da tattaunawa da hukumomin tsaro kuma har zuwa sanda zasu bamu tabbaci matakin zai cigaba da kasancewa."
"Sakamakon da muke samu daga hukumomin tsaro, shine zai tabbatar da lokacin da zamu ɗage hanin."

Gwamnatin Katsina ta datse sabis a wasu yankuna

Gwamnatin jihar Katsina ta datse hanyoyin sadarwa a ƙananan hukumomi 13 na jihar, waɗanda ake ganin ayyukan yan bindiga ya fi muni a yakunansu.

Kara karanta wannan

Ba zan sake afuwa gare ku ba, gwamnan arewa ga ‘yan bindiga, ya sha alwashin hukunta masu daukar nauyinsu

Kananan hukumomin sun haɗa da Funtua, Malumfashi, Bakori, Dutsin-ma, Faskari, Sabuwa, Dandume, Safana, Batsari Kankara, Danmusa, Jibia da kuma Kurfi.

Jiragen yakin Super Tucano suna kan hanya

A wani labarin kuma Ruwan Bama-Bamai Ba Kakkautawa yayin da Kashi Na Biyu Na Jiragen Yaƙin A-29 Super Tucano Suka Nufo Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa jiragen yaƙi guda 6 ƙirar A-29 Super Tucano da Najeriya ta siya daga Amurka sun taho Najeriya.

Tun a watan Fabrairun 2018 ne gwamnatin Najeriya da siya jiragen guda 12 kan kudi dala miliyan $496m.

Asali: Legit.ng

Online view pixel