Da dumi-dumi: Daliban Zamfara 75 da aka sace sun samu 'yanci bayan kwanaki 11

Da dumi-dumi: Daliban Zamfara 75 da aka sace sun samu 'yanci bayan kwanaki 11

  • An kubutar da daliban da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka sace su daga wata makarantar gwamnati a jihar Zamfara
  • Babu wanda ya saki cikakken bayani kan yadda aka saki yaran tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da rundunar 'yan sandan Najeriya
  • Ku tuna cewa a ranar Laraba, 1 ga watan Satumba ne 'yan bindiga suka mamaye makarantar suka fara harbi ba kakkautawa kafin suka sace daliban

Gusau, Zamfara - Wani rahoton gidan talabijin na Najeriya (NTA) ya nuna cewa dalibai 75 na Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Kaya da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara da ‘yan bindiga suka sace sun samu ‘yanci.

NTA ta wallafa a Facebook:

"Dalibai saba'in da biyar na Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Kaya da ke Karamar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara sun sake samun 'yanci."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: An toshe hanyoyin sadarwa na zamani a jihar Katsina

An yi garkuwa da daliban ne da safiyar Laraba, 1 ga watan Satumba, lokacin da ‘yan bindiga suka mamaye makarantar sannan suka fara harbi ba kakkautawa kafin suka kwashe daliban da wani malami.

Da dumi-dumi: Daliban Zamfara 75 da aka sace sun samu 'yanci bayan kwanaki 11
Daliban Zamfara 75 da aka sace sun samu 'yanci bayan kwanaki 11 Hoto: AUDU BULAMA BUKARTI
Asali: Facebook

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a sanar da cikakken bayani kan yadda aka sako daliban ba ko kuma an biya kudin fansa don sakin nasu ba.

Daily Trust ta rawaito cewa wannan ci gaban ya zo ne bayan an katse hanyoyin sadarwa a Zamfara a matsayin hanyar magance matsalar ‘yan fashi.

Dalibai 5 cikin 73 da aka sace a Zamfara jiya sun kubuta

A baya mun kawo cewa dalibai biyar cikin wadanda aka sace 73 ranar Laraba a makarantar gwamnatin GDSS Kaya, dake karamar hukumar Maradun, jihar Zamfara, sun samu kubuta.

Kara karanta wannan

‘Yan banga 5 sun hadu da ajalinsu sakamakon harin ‘yan bindiga a hanyar Birnin Gwari

The Punch ta ruwaito cewa tsohon Kansilan gundumar Kaya, Yahaya Kaya, ya tabbatar da kubutar yaran ranar Alhamis. Yace diyarsa, Amina, na cikin wadanda suka samu kubuta daga hannun yan bindigan.

A cewarsa, an mayar da daliban garinsu Kaya, misalin karfe 1 na dare. Yace suna cikin koshin lafiya.

Zamfara: Iyayen daliban da aka sace sun shiga mawuyacin hali bayan katse layukan waya

Legit.ng ta kuma kawo cewa Iyayen daliban da aka sace daga Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Kaya, karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara, sun koka kan rashin iya jin ta bakin masu garkuwa da mutanen da suka sace 'ya'yansu.

Rundunar ‘yan sanda ta ce an sace dalibai 73 lokacin da 'yan bindiga suka mamaye makarantar da misalin karfe 11 na safiyar Laraba da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel