Bayan katse hanyoyin sadarwa, mun damƙe masu kaiwa yan bingida bayanai 2,000 a Zamfara, Kwamishina

Bayan katse hanyoyin sadarwa, mun damƙe masu kaiwa yan bingida bayanai 2,000 a Zamfara, Kwamishina

  • Kwamishinan yaɗa labarai da Al'adu na jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Dosara, yace ɗauke sabis a Zamfara ya haifar da ɗa mai ido
  • Dosara yace zuwa yanzun hukumomin tsaro sun samu nasarar damke yan leken asirin yan bindiga sama da 2,000 cikin kwana 30
  • Hakanan yace gwamnatin jihar zata dawo da sabis ɗin sadarwa a babban birnin jihar, Gusau, kafin ƙarewar wannan makon

Kaduna - Sama da yan leken asirin yan bindiga 2,000 aka cafke a jihar Zamfara sanadiyyar datse hanyoyin sadarwa a jihar, a cewar kwamishinan yaɗa labarai, Alhaji Ibrahin Dosara.

Kwamishinan ya bayyana haka ne a jihar Kaduna, yayin da yake jawabi game da Operation ɗin sojoji a jihar Zamfara, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Yace an tsananta bincike kan waɗanda ake zargi da leken asirin domin su faɗi masu ɗaukar nauyinsu da kuma abokan aikinsu.

Read also

Ta fashe: Sirrin kazamar dukiyar shugabannin duniya 35, 'yan siyasa 330 da biloniyoyi 130 a kasashe 91

Dauke sabis a Zamfara
Bayan katse hanyoyin sadarwa, mun damƙe masu kaiwa yan bingida bayanai 2,000 a Zamfara, Kwamishina Hoto: channelstv.com
Source: UGC

A cewarsa, wasu daga cikin waɗanda suka shiga hannu, sun faɗi sunayen wasu manyan mutane dake ɗaukar nauyin su.

Ya ƙara da cewa hukumomin tsaro na aiki kan bayanan da suka samu daga hannun mutanen domin kame waɗanda suke haɗa kai da su.

An hallaka yan fashi da dama - Dosara

Alhaji Dosara ya ƙara da cewa hukumomin tsaro sun samu nasarar hallaka yan bindiga da yawan gaske yayin da wasu suka tsere zuwa jihohin dake makwabtaka, kamar Sokoto da Katsina.

Dosara yace:

"Mun samu nasarori da dama a wata daya da ya gabata, domin yan bindiga sun tsere zuwa jihohin Katsina da Sokoto."
"Jiya jiyan nan kwamishinan yan sanda na jihar Sokoto yace kashi 80% na yan bingidan Zamfara sun shiga Sokoto yayin da ragowar kashi 20% suka tsere Katsina."

Read also

Tsohon Sarki Sanusi ya soki tsarin biyan tallafin fetur, ya fallasa badakalar da ke cikin tsarin

"Zuwa yanzun jami'an tsaro sun cafke yan leken asiri 2,000 kuma suna cigaba da tsananta bincike kansu, sun faɗi sunayen waɗanda suke haɗa kai da su, cikinsu har da manyan mutane."

Shin gwamnati ta san halin da jama'a suka shiga?

Kwamishinan yace gwamnatin Zamfara tana sane da matsanancin halin da jama'a suka shiga saboda datse sabis ɗin sadarwa.

An ɗauki matakin ne domin share yan bindiga daga jihar, ba don a jefa yan jihar cikin wani hali ba, a cewarsa.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Zamfara zata maida hanyoyin sadarwa a Gusau, babban birnin jihar, kafin ƙarshen makon nan, kamar yadda Premium times ta ruwaito.

A wani labarin na daban Ka gaggauta ayyana yan fashin daji a matsayin yan ta'adda, Majalisar wakilai ga Shugaba Buhari

Majalisar wakilan tarayya ta bi bayan majalisar dattijai wajen kira ga shugaba Buhari ya ayyana yan fashi a matsayin yan ta'adda, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Read also

'Yan bindiga sun sheke ma'aikacin jinyan MSF da wasu mutum 2 a Zamfara

A zaman majalisar na ranar Alhamis, shugaban kwamitin tsaro, Babajimi Benson, ya gabatar da bukatar goyon bayan matakin sanatoci cikin gaggawa.

Source: Legit

Online view pixel