Attahiru Bafarawa: Mutane sun shiga bala'i a yankin Arewa musamman a Zamfara

Attahiru Bafarawa: Mutane sun shiga bala'i a yankin Arewa musamman a Zamfara

  • Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, ya nuna damuwarsa kan halin da al'ummar yankin arewa maso yamma suke ciki
  • Bafarawa yace matsalar tsaro ta kai yadda manoma sun kasa zuwa gonakinsu girbin abinda suka noma saboda tsoron yan bindiga
  • Ya yi kira ga gwamnan Zamfara da kuma shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, su rinka ziyara zuwa jihohin wannan yanki don ganewa idonsu

Zamfara - Tsohon gwamnan Sokoto, kuma sanannen ɗan siyasa, Attahiru Bafarawa, yace mutane sun shiga cikin matsin rayuwa a yankin arewa maso yamma.

Bafarawa ya koka kan yanda mutane suka sha wahalar noma amfanin gona amma matsalar tsaro ta hana su zuwa ɗebo abinda suka noma.

Ya kuma ƙara da cewa halin da mutane suka tsinci kansu a yankin Arewa maso yamma musamman Sokoto da Zamfara, ba ya misaltuwa domin ya wuce tunani.

Kara karanta wannan

Dalilin Na Yasa Muka Nemi Afuwar Yan Najeriya Kan Yadda Muka Gudanar Da Mulki, Aisha Buhari

BBC Hausa ta ruwaito tsohon gwamnan ya bukaci gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya kai ziyara zuwa wasu sassan jiharsa domin ganin halin da mutane ke ciki.

Attahiru Bafarawa
Attahiru Bafarawa: Mutane sun shiga bala'i a yankin Arewa musamman a Zamfara Hoto: lindaikejisblog.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakazalika ya gane wa idonsa irin tasiri ko akasin haka na matakan da ya ɗauka don magance ayyukan tsagerun yan bindiga.

Ko ana faɗa wa shugaban ƙasa halin da mutane ke ciki?

Bafarawa ya bukaci shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya kai ziyara waɗannan jihohi ko kuma ya tura amintattunsa domin su gano ainihin abinda ke faruwa.

Tsohon gwamnan yace:

"Ban sani ba makusantan shugaba Buhari suna faɗa masa gaskiyar abinda ke faruwa a jihohin arewa, idan basu faɗar gaskiya to sun cuce mu."
"Ni ganau ne, manoma na cikin bala'i, domin a halin da ake ciki yanzun suna tsoron zuwa girbin abinda suka noma saboda matsalar tsaro."

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Dakatar Yakin Neman Zabe Kan Abu Ɗaya Da Ya Shafi Yan Najeriya

Shin dagaske gwamnati na tallafawa mutane da Abinci?

A cewar tsohon gwamnan, shi dai bai taɓa ganin hakan ba, kuma yana zuwa Bafarawa lokaci bayan lokaci amma ko labarin tallafin bai taɓa ji ba.

"Ya kamata idan shugaba ya kafa doka, to ya sanya kwamiti da zai rinka sa ido wajen tabbatar da dokar na aiki, ko kuma shi dakansa ya rinka bibiyar lamarin."
"Idan ka bada umarnin a tallafawa mutane da abinci, a matsayinka na shugaba kamata ya yi ka sa a rinka duba ko tallafin na kaiwa ga al'umma ko baya zuwa."

A wani labarin na daban kuma Manoma Sama da 20 Sun Mutu, Yayin da Jirgin Yaki Ya Yi Kuskuren Sakin Bama-Bamai a Borno

Aƙalla mutanen ba basu ji ba basu gani ba 20 sun rasa rayukansu sanadiyyar harin jirgin yaƙi a Dabar Masara, ƙaramar hukumar Monguno, jihar Borno, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Peter Obi Ya Gana da Wani Gwamnan Arewa, Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Tinubu, Atiku da Kwankwaso

A cewar wata majiya daga yankin, harin saman ya faru ne ranar Lahadi, 26 ga watan Satumba da yammaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262