Farashin Buhun Siminti a Najeriya Ya Fi Sauran Kasashen Afrika har Gwamnati Ta Shiga bincike
- An gano cewa farashin siminti a Najeriya ya fi na makwabtan kasashe tsada nesa ba kusa ba duk da irin wadatar kasar
- Hukumar FCCPC ta gayyaci manyan kamfanonin siminti domin su bayyana mata yadda suke kayyade farashin kayansu
- Shugaban hukumar, Tunji Bello, ya ce hauhawar farashin siminti na yi wa ci gaban tattalin arziki da gina muhalli zagon kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Sakamakon wani bincike da hukumar FCCPC ta gudanar ya nuna yadda ake fama da tsadar siminti a Najeriya.
Kudin buhun siminti a cikin Najeriya ya zarce farashin da sauran makwabtan Najeriya suke sayan kayan a kasuwanninsu.

Source: Facebook
Akwai yiwuwar yaudara a kasuwar siminti
Rahoton da aka samu daga The Nation ya ce akwai yiwuwar cewa wasa da kasuwa da ake yi ne ya jawo siminti ya yi tsada.

Kara karanta wannan
Cutar Apollo ta ɓarke a wasu jihohin Arewacin Najeriya, ta fara yaɗuwa cikin jama'a
Masana da ‘yan kasuwa da masu ilmin tattalin arziki sun ce abubuwan da suka jawo tashin farashin suna da daure kai sosai.
Hakan ya jawo FCCPC da ke da alhakin tsare masu sayen kaya ta tashi tsaye bayan alkawuran rage kudi sun ki aiki har yau.
Siminti ya yi tsada a Najeriya mai arzikin Limestone
Binciken ya duba yadda Najeriya ta ke da arzikin Limestone, adadin al’umma, karfin hada siminti, bukatarsa da kuma farashin sari.
Hukumar FCCPC mai kare masu sayen kaya a Najeriya ta fitar da wani dogon rahoto mai tsawon shafi 40 a karshen binciken nata.
Duk da tulin sinadarin Limestone da kasar nan ta mallaka, farashin buhun siminti yana ta tashi a kasuwa a halin yanzu.
Nawa ake saida siminti a Najeriya & sauran kasashe?
An shigo shekarar nan ana saida buhun siminti mai cin kilo 50 a kan kimanin N9, 300 amma yanzu yana kai har N15, 000.
A watan Yulin nan, an saida buhun daga N13, 000 zuwa N15, 000 a garuruwan Najeriya.
Hukumar ta ce a kasar Kenya kuwa, farashin buhu yana kan N7, 344 ne idan aka yi lissafi da farashin dala a kasuwar canji.
A kasar Tanzaniya kuwa, jaridar Punch ta rahoto cewa siminti bai wuce N6, 500. A kasuwannin Togo kuma ya ka kai N9, 180.
Me ya jawo tsadar siminti a Najeriya?
Sabanin da aka samu ya nuna arzikin da Najeriya ta ke da shi da karfin kamfanonin simintin ba su kawo wa jama’a sauki ba.
An gano abubuwan da suke jawo tsadar sun hada da faduwar Naira, tsadar kudin wuta da kudin sufuri da na shigo da sauran kaya.
Kudin wutar lantarki da farashin dala sun tashi sakamakon cire tallafi da gwamnati ta yi a 2023.
FCCPC za ta binciki kamfanonin siminti
FCCPC za ta duba ta gani ko tashin farashin na tsakani da Allah ne ko kuma sharrin ‘yan kasuwa ne kawai ya jawo hakan.
An fara gayyatar masu ruwa da tsaki a harkar ana neman bayanin yadda suke tsaida farashi, buga siminti da fitar da kaya.
Binciken zai kuma duba alakar da ke tsakanin ‘yan kasuwa da nufin ganin farashin buhun simintin ya rage kudi a Najeriya.
Shugaban FCCPC, Tunji Bello ya ce hakan ya zama dole saboda muhimmancin siminti ga tattalin arziki da cigaban kasa.
Akuyar da ta zama silar arzikin sanata
Kuna da labari Dino Melaye ya ce dukiyarsa ta fito ne daga kiwon akuya da ya fara yana dan shekara 12, lokacin yana sakandare.
Da wannan akuya ta haihu ne sai ya samu kudin biyan kudin makarantarsa, sannan ya zuba sauran kudin a harkar hannun jari na duniya.
Tsohon sanatan yammacin Kogi ya bayyana yadda wannan akuya da ya saya ta buda masa hanyar da a yau yana da motoci fiye da 200.
Asali: Legit.ng

