Matawalle: Mun daina tattaunawa da 'yan bindiga saboda sun yaudare mu

Matawalle: Mun daina tattaunawa da 'yan bindiga saboda sun yaudare mu

  • Matawallen Maradun, gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad ya ce tuni ya sauya shawarar sasanci da 'yan bindiga
  • A cewarsa, miyagun mayaudara ne, don haka ba zai sake karbar tubarsu ba balle a yi musu rangwame a Zamfara
  • Ya bayyana cewa, luguden wutar da ake musu ya na haifar da da mai ido saboda an samu saukin kashe jama'a da sace su

FCT, Abuja - Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara, ya ce jiharsa ta canza shawararta kan tattaunawa da 'yan bindiga saboda yaudarar gwamnatinsa da suka yi.

A baya, Matawalle ya sanar da cewa tattaunawa ce kawai hanyar da ta dace wurin yakar lamurran 'yan bindiga a kasar nan, TheCable ta ruwaito.

Matawalle: Mun daina tattaunawa da 'yan bindiga saboda sun yaudare mu
Matawalle: Mun daina tattaunawa da 'yan bindiga saboda sun yaudare mu. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Har ila yau, yayi kira ga takwarorinsa da su mayar da hankali wurin tattaunawa da 'yan bindigan domin samar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda da 'yan bindiga sun mamaye murabba'in mita 1,129 na gandun dajin Najeriya

Amma yayin halartar sallar Juma'a ta ranar goma ga watan Satumba, gwamnan ya ce jiharsa ba za ta sake yi wa tubabbun 'yan bindiga rangwame ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin jawabi ranar Alhamis wurin amsa tambayoyin manema labaran gidan gwamnati bayan taron da yayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Aso Villa, Matawalle ya ce a yanzu akwai zaman lafiya a jiharsa.

Ya ce gwamnatin jihar ta mayar da hankali wurin yaki da 'yan fashin daji, inda ya kara da cewa matakan da aka dauka na samar da zaman lafiya suna aiki, TheCable ta wallafa.

"Sun yaudare mu. Wasu daga cikinsu ba su bi yarjejeniyar da muka yi ba. A tunaninmu abu ne da za mu iya cigaba tare da su, amma daga baya muka gane cewa yaudara ce. Hakan yasa muka janye muka yanke hukuncun yakar su," yace.

Kara karanta wannan

An bankado sabbin mafakar ‘yan bindigar Zamfara da ke tserewa

"Kamar yadda kuka sani, muna yakarsu kuma mun dauka matakai masu yawa domin dakile cigaban al'amarin. Muna godiya ga Ubangiji da yasa mu ke ganin sakamako. Mun samu nasarori masu tarin yawa a abinda mu ke yi.
"Kamar yadda ku ka sani, akwai jami'an tsaro masu tarin yawa da aka tura jihar Zamfara kumar suna aiki babu wasa."

A kan halin da jihar ta ke ciki, Matawalle ya ce akwai zaman lafiya kuma jama'a na cigaba da harkokinsu.

"Kawai dai mun datse abubuwa masu yawa, daga yawo da kayan abinci, dabbobi da kuma siyar da kayayyakin man fetur," yace.
"Mun saka matakai masu yawa kuma jama'a suna farin ciki da matakan saboda an wahala da yawa. Ana kashe mutane tare da sace su a kowacce rana, amma a yau mun yi nasara. Ba mu da matsala a jihar Zamfara."

Majalisar jihar Kano ta amince da bukatar Ganduje ta karbo bashin N4bn

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

A wani labari na daban, majalisar jihar Kano ta amince wa gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya karbo bashin N4 biliyan da ya ke nema domin kammala ayyukan wutar lantarki na Tiga da Challawa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, an amince da karbo bashin ne yayin zaman majalisar wanda ya samu shugabancin kakakin majalisar jihar Kano, Ibrahim Chidari.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da aka mika wa daraktan yada labarai na majalisar, Uba Abdullahi, wanda ya ce majalisar ta zauna kan al'amarin bayan kakakin ya karantowa majalisar da gwamnan ya tura musu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel