Siyasar Najeriya
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC reshen jihar Neja, ta karbe tikitin takarar kujerar wakilin shiyyar Neja ta Gabas na majalisar dattawa daga hannu Sanata David Umaru ta kuma danka shi a hannun Muhammad Sani Musa.
A ranar Asabar, 16, ga watan Fabrairun 2019, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ta dage babban zaben kasa na shugaban kasa da kuma na 'yan majalisar tarayya zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu na shekarar da muke ciki.
Jigo a jm’iyyar PDP kuma Tsohon na hannun damar shugaban kasa Buhari a jam’iyyar ANPP da CPC, Buba Galdima, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai iya cin zaben shugaban kasa ba ko da kuwa ubangiji ne zai kirga kuri’u. Galadi
A jiya, Asabar, ne shugaban hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya amsa cewar sanatan jam’iyyar APC mai wakilta jihar Neja ta gabas, Sanata Mohammed Musa, na daga cikin ‘yan kwangilar hukumar. Shugaban na
Mun samu cewa, daga karshe gwamnatin kasar Amurka ta yi furuci na tofa albarkacin bakin ta dangane da dage babban zaben kasa da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta yi a jiya Asabar, 16, ga watan Fabrairun 2019.
Tijanniyah tsari ne na sufanci ba kungiya ba. Tijaniyah ba ta tilastawa mabiyanta zaban wani dan takara ba," inji Maqari. Abinda shugabanin Tijyaniyah suka ce shine mabiyansu su zabi shugabani masu gaskiya da rikon amana, halaye
Anan tsohon gwamnan jahar Kano Malam Ibrahim Shekarau, kuma tsohon dan takarar shugabancin Najeriya, wanda a yanzu haka yake takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, ne ya shirya addu’o’i na musamman.
“Ka dawo da martabar Najeriya ta kyakkyawar shugabanci, don haka zamu cigaba da baku goyon baya a tsare tsare da kuma shirye shiryen da gwamnatinka da take yi ma yan Najeriya wadanda zasu kai kasar ga gaci.” Inji Sarkin Farouk.
A yau Alhamis, 14, ga watan Fabarairu, ta yi daidai da ranar da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta kayyade domin kowane dan takarar kujerar shugaban kasa ya rufe taron sa na yakin neman zabe da za a gudanar a jibi.
Siyasar Najeriya
Samu kari