A Karshe, INEC Ta Yi Matsaya kan Takarar Atiku da 'Yan ADC a 2027

A Karshe, INEC Ta Yi Matsaya kan Takarar Atiku da 'Yan ADC a 2027

  • INEC ta sanar da cewa za ta amince da 'yan takarar da bangaren David Mark ya amince da su a jam'iyyar ADC
  • Hukumar zaɓe ta bayyana cewa ADC ta riga ta fitar da 'yan takara 471 da suka hada da matakin shugaban kasa
  • ADC ta bukaci a yi bincike tare da gurfanar, Nafiu Bala kan fitowa karara ya ce ya sanya sunayen 'yan takara a shafin INEC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) ta tabbatar da cewa za ta jam'iyyar ADC da Sanata David Mark ke jagoranta a zaɓen 2027.

Kwamishinan INEC, Mohammed Haruna, ne ya yi karin bayani game da batun daura sunayen 'yan takarar ADC a safin hukumar domin shiga zaben 2027.

Kara karanta wannan

Kotu ta hana tilasta wa ɗan jarida fallasa majiyoyinsa a shari'ar Ganduje

Atiku Abubakar a wajen taro
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar. Hoto: Paul O. Ibe
Source: Facebook

Mohammed Haruna ya fitar da bayanin ne yayin wata hira ta musamman da ya yi da jaridar Punch, inda ya ce za su aiki da hukucin kotu kan jam'iyyar ADC.

INEC za ta amince da Atiku

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za ta amince ne kawai da 'yan takarar da shugabancin jam'iyyar ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark ya miƙa,

INEC ta yi magana tana mai tabbatar da cewa wannan ɓangaren jam'iyyar ya riga ya gabatar da sunayen 'yan takara 471 domin zaɓen gama gari na 2027.

Kwamishinan INEC, Mohammed Haruna, ya shaida cewa hukumar ta bai wa ɓangaren David Mark damar shiga tsarin gabatar da sunayen 'yan takara bayan hukuncin Kotun Ƙoli da ya tabbatar da shugabancinsa.

A bayanin da ya yi, Mohammed Isa ya ƙara da cewa ɗayan ɓangaren jam'iyyar na Nafiu Bala ba shi da hurumin doka na gabatar da 'yan takara.

Kara karanta wannan

"Tinubu zai sha kaye," An yi hasashen gwamnan da zai lashe zaben shugaban ƙasa a 2027

Farfesa Joash Amupitan
Shugaban hukumar zabe, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

A hirar da ya yi, kwamishinan INEC ya ce:

“Eh, mun bai wa ɓangaren David Mark lambar shiga tsarin ne bisa hukuncin Kotun Ƙoli da ya tabbatar da shugabancinsa a jam'iyyar.
"Tun daga lokacin wannan ɓangaren ya gabatar da mafi yawan 'yan takararsa guda 471, waɗanda suka haɗa da 'yan takarar shugaban ƙasa, sanatoci 109 da kuma 'yan takarar Majalisar Wakilai 360.
“Kotun ba ta ce mu karɓi sunayen 'yan takarar da wani ɓangaren jam'iyyar ya gabatar ba, musamman ma kasancewar wannan ɓangaren ya rasa nasara a ƙarar da ya shigar domin neman amincewa da shi.”

An bukaci kama Nafiu Bala

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta buƙaci a binciki tare da gurfanar da shugaban tsagin ɓangaren jam'iyyar, Nafiu Gombe, bayan INEC ta bayyana ta karyata iƙirarinsa.

Rahotanni sun nuna cewa Nafiu Bala ya yi ikirarin cewa ya sanya sunayen 'yan takarar jam'iyyar na zaɓen 2027 ta hanyar tsarin hukumar zabe mai zaman kanta.

Da yake martani ga bayanin INEC, kakakin jam'iyyar ADC ya ce ya yi maraba da matsayin hukumar, tare da zargin Nafiu Bala da ƙoƙarin yaudarar 'yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng