Hanga Ya Yi Magana kan Amsa Gayyata bayan APC Ta Nemi Ya Rabu da Kwankwaso

Hanga Ya Yi Magana kan Amsa Gayyata bayan APC Ta Nemi Ya Rabu da Kwankwaso

  • Sanata Rufa'i Sani Hanga mai wakiltar Kano ta Tsakiya ya ce tun daga kafuwar tafiyar Kwankwasiyya ya kasance mai biyayya gare ta har zuwa yanzu
  • Sai dai ya bayyana cewa duk da makauniyar biyayya da ya yi, ya ji labari Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce ai shi na gida ne, saboda haka a yi hakuri
  • Amma Sanatan ya bude kofar sauya sheka, inda ya bayyana cewa duk da ba shi da niyyar amsa wata gayyata a yanzu, amma akwai abin da zai kore shi a NDC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufa'i Sani Hanga ya bayyana cewa ya yi wa tafiyar Kwankwasiyya biyayya tun daga lokacin da aka fara ta kuma ya yi biyayya a 'makance'.

Kara karanta wannan

Kalaman Sanata Graham na karshe sun bayyana kafin mutuwarsa a Amurka

Ya ce duk da matsayinsa, gogewarsa da shekarunsa, ya yanke shawarar kasancewa mai biyayya ga Kwankwasiyya, kuma har yanzu yana kan wannan tsari.

Sanata Hanga ya yi magana bayan tayin APC
Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sanata Rufa'i Sani Hanga Hoto: Sadiq Nahaja, Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

A hirar da ya yi da Dan Uwa Rano TV, wadda aka wallafa a shafinta na Facebook, Sanata Hanga ya yaba wa magoya bayansa bisa haƙurin da suka nuna bayan rashin samun tikitin takara da ya yi.

Sakon Hanga ga masoyansa

Sanata Rufa'i Sani Hanga ya bayyana cewa gaba ta fi baya yawa, saboda haka ya roƙi magoya bayansa su yi haƙuri da halin da ake ciki a yanzu.

A cewarsa:

"Ina ta yi masu bayani yanzu su yi haƙuri, saboda gaba ta fi baya yawa. In Sha Allah ba za su yi da-na-sani ba kan wannan abu da ya same ni na rashin takara."

Ya ƙara da cewa yana da hanyoyin makoma da dama, saboda haka bai kamata magoya bayansa su damu da rashin samun tikitin takarar da ya yi a jam'iyyar NDC ba.

Hanga ya yi magana kan kiran APC

Sanatan ya ƙara da cewa zuwa yanzu bai yanke shawarar shiga wata jam'iyya ba, duk da kiran da jam'iyyar APC ta yi masa da ya rabu da tafiyar Kwankwasiyya.

Kara karanta wannan

"Ba boyewa na yi ba"; Adeyemi ya bayyana abin da yake tsoro kan badakalar PFIPC

Hanga ya ce ba shi da niyyar amsa gayyata a yanzu
Sanata Rufai Sani Hanga a zauren majalisar dattawa a Abuja Hoto: The Nigerian Senate
Source: Twitter

Sanata Rufa'i Sani Hanga ya ce:

"A'a, ni ba wannan ne a gabana ba. Ba na shirya amsa goron gayyata. Ina ka ji na amsa goron gayyata na ce ga ni? Wata kila an kore ni daga inda nake ko kuma an rufe ƙofa."

Ya ce mutane ne kawai suke ganin an yi masa kira da muhimmanci, kuma zai fara nazari domin fahimtar halin da ake ciki a jam'iyyar NDC kafin ya yanke hukunci.

Sanatan ya ce magoya bayansa ba za su yi fushi da shi ba, sai dai idan sun ba shi shawara kan yadda za a samar musu mafita amma ya ƙi amincewa.

Sai dai ya buɗe ƙofar sauya sheka, inda ya tabbatar da cewa idan magoya bayansa suka zo masa da hujjoji masu ƙarfi, zai iya jagorantarsu zuwa duk jam'iyyar da suka zaɓa.

Hanga ya yi magana kan zaben 2027

A baya, mun wallafa cewa Sanatan Kani ta Tsakiya, Rufai Sani Hanga ya yi hasashen faduwar jam’iyyar hammayarsu wato NDC a zaben shugaban kasa da za a yi a 2027 a wasu jerin kalamai masu kama da na 'yan adawa.'

Kara karanta wannan

"Atiku ake so": Jigo a APC Kano ya yi tir da tikitin Muslim Muslim

Ko da jam’iyyar hamayyar ta tsaida Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, sanatan na Kano ya fi ganin nasarar jam'iyyar hadakar yan adawa ta ADC da ta tsayar da Alhaji Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi.

Sanata Hanga ya ce rashin tsaro da kuncin rayuwa da ake fama da shi za su iya yi wa Bola Tinubu illa wajen neman tazarce kuma hakan zai ba wa Atiku Abubakar na ADC damar lashe babban zaben da ke tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng