Abin da ya sa bai kamata a ba Ibo takarar Shugaban kasa a 2023 ba – TNN

Abin da ya sa bai kamata a ba Ibo takarar Shugaban kasa a 2023 ba – TNN

Shugaban kungiyar Unity Forum ta tafiyar Tinubu-Not-Negotiable 2023, Mutiu Okuola, ya yi karin haske game da shirye-shiryen zabe mai zuwa.

Mista Mutiu Okuola ya yi hira da wata fitacciyar jarida inda ya bayyana dalilinsu na marawa Bola Tinubu baya a matsayin ‘Dan takarar shugaban kasa.

Mutiu Okunola ya bayyana cewa maganar da wasu ke yi na cewa Arewa za ta cigaba da mulkin Najeriya har bayan 2023 bai samu karbuwa a Yankin ba.

Shugaban wannan tafiya ya nuna cewa wasu tsirarru ne kurum ke kokarin ganin ‘Yan Arewa sun cigaba da mulki domin su samu hanyar sace dukiyar kasa.

A game da mika takarar shugaban kasa ga Ibo, Okunola ya na ganin cewa yanzu sai da a rika maganar Arewa ko Kudu, amma ba a gutsura yankunan ba.

KU KARANTA: Jagororin Jam’iyya 44 sun hadu sun tsige Shugaban PDP a Jihar Kano

Okunola ya ke cewa a siyasa babu wanda zai ba mutanen Kudu maso Gabas mulki a bagas, duk da cewa sun cancanci su rike mulkin Najeriya a 2023.

‘Dan siyasar ya kara da cewa: “Idan jam’iyyar APC ta ajiye banbanci a gefe guda, ta ba yankin da ba su da karfi takara, hakan ba zai yi wani aiki ba.”

"Ku sani cewa ba mu da gwamna ko guda a jihohin Kudu maso Gabas da su ke son mulki, ba za mu kai labari ba, domin PDP ce ke da karfi a Yankin.”

A hirar ta sa, Okunola ya bayyana cewa tsohon gwamna Bola Tinubu ne ya dace da takara daga Kudu domin ya cancanta saboda mukaman da ya rike.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel