Mutuwar Sanata Graham: Trump Ya Aika Sako ga Hukumar FBI da Ke Shirin Bincike
- Shugaba Donald Trump na Amurka ya aika sako ga hukumar FBI kan binciken rasuwar Sanata Lindsey Graham
- Trump ya bayyana cewa Graham ya rasu ne sakamakon matsalar lafiya, yana mai cewa mahaifinsa ma ya mutu sakamakon bugun zuciya
- Rahotanni sun nuna Graham ya yi korafin ciwon ƙirji kafin rasuwarsa, yayin da bincike ya nuna tsagewar babban jijiyar jini ce ta yi sanadin mutuwarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi magana kan hukumar FBI game da binciken mutuwar Sanata Lindsey Graham.
Trump ya ce FBI na ɓata lokacinta idan tana binciken jita-jitar da ke cewa akwai wata makarkashiya a bayan rasuwar Sanata Lindsey Graham.

Source: Facebook
Trump ya bayyana haka ne a Fadar White House lokacin da wani ɗan jarida ya tambaye shi dalilin da ya sa FBI ke taimakawa wajen binciken lamarin, cewar CBS News.
Trump na mamakin FBI kan mutuwar Graham
Shugaban ya ce bai san dalilin da ya sa FBI ke shiga binciken ba, yana mai jaddada cewa Graham ya rasu ne saboda matsalar lafiya da ta shafi zuciya.
Ya ƙara da cewa mahaifin Sanata Graham ma ya mutu sakamakon bugun zuciya yana da shekaru 69, abin da ya nuna akwai tarihin irin wannan cuta a iyalinsu.
Sakamakon binciken farko na likitocin binciken gawar ya nuna cewa Graham ya mutu ne saboda tsagewar babban jijiyar jini da ke fitar da jini daga zuciya.
Trump ya ce yana fatan marigayin ya fi kula da lafiyarsa, yana mai bayyana cewa irin wannan matsalar ba ta da sauƙin ganowa tun kafin ta tsananta.
Shugaban ya kuma ce likitocin Fadar White House sun yi masa bayanin yadda ake samun wannan cuta da kuma yadda ta iya haddasa mutuwar Graham.

Source: Getty Images
Abin da ya yi sanadiyar Sanata Graham
Majiyoyi da dama sun shaida wa cewa Graham ya koka da ciwon ƙirji jim kaɗan kafin rasuwarsa bayan dawowarsa daga wata tafiya zuwa Ukraine.

Kara karanta wannan
PFIPC: Kamfanin Amurka ya kawo ɗauki ga shugaban hukumar bogi da ake ta surutu a Najeriya
Saboda matsayinsa mai tsauri kan Rasha da Iran, wasu mutane sun riƙa yaɗa hasashen cewa wata ƙasa ce ke da hannu a mutuwarsa, cewar Fox News.
Sai dai Trump ya yi watsi da waɗannan jita-jita, yana mai cewa bai ga wata alamar mugun nufi ko makarkashiya a rasuwar Graham ba.
Ya ce ana ta yaɗa ra'ayoyin ƙage a kafafen sadarwa, kuma idan FBI na binciken waɗannan zarge-zargen, to tana ɓata lokacinta ne.
Daraktan FBI Kash Patel ya bayyana cewa hukumar tana taimakawa hukumomin yankin kawai wajen gudanar da binciken da ya shafi rasuwar Sanata Lindsey Graham.
Yadda Sanata Graham ya rasu
An ji cewa Sanata Tommy Tuberville ya yi magana game da kalaman marigayi Lindsey Graham ya yi kafin mutuwarsa a kasar Amurka.
An ce Graham bai kira lambar gaggawa ta 911 ba, sai ma'aikaciyarsa ta yi hakan, inda jami'an ceto suka same shi cikin mawuyacin hali.
Rahotanni sun ce Graham ya jinkirta neman kulawar likita saboda yana son kammala wasu muhimman ayyukan siyasa da suka shafi Rasha, Iran.
Asali: Legit.ng
