Abba Ya Shiga Ya Fita, APC na Shirin Raba Kwankwaso da Sanata Hanga
- Rahoto ya nuna cewa jam'iyyar APC ta buƙaci Sanata Rufai Sani Hanga ya sauya sheƙa zuwa cikinta daga NDC
- Jam’iyyar ta zargi Rabiu Musa Kwankwaso da wulakanta Sanata Hanga tare da mayar da shi saniyar ware a yanzu
- APC ta ce ƙin ba Hanga wata takara a NDC ya nuna cewa ba a ƙara ganin darajarsa duk da tasirinsa a siyasar Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta ƙara ƙaimi wajen jan hankalin Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufai Sani Hanga, domin ya koma cikinta.
APC ta yi magana tana mai cewa jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya wulakanta shi tare da mayar da shi saniyar ware.

Source: Facebook
Legit Hausa ta gano cewa hadimin Abba Kabir Yusuf, Ibrahim Adam ya wallafa a Facebook cewa tawagar APC ta zauna da Sanata Hanga.

Kara karanta wannan
'A zagi Kwankwaso kai tsaye:' NDC ta mayar wa Sanata Hanga martani kan takarar Kano
APC ta je zawarcin Hanga
APC ta fara zawarcin Sanata Hanga ne a ranar Talata lokacin da wata tawagar manyan jam'iyyar ta gana da shi.
Jam'iyyar, a ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban APC na Jihar Kano, Salisu Maje Gwangwazo, ta kai masa ziyarar gaisuwa a gidansa bayan dawowarsa daga tafiyar jinya.
Da yake jawabi ga Sanata Hanga, Gwangwazo ya ce ya kamata a ba shi kulawa da girmamawa fiye da yadda aka yi masa, la’akari da dogon lokacin da ya shafe yana nuna biyayya da kuma sadaukarwa ga Kwankwaso.
Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin siyasa game da makomar Hanga, bayan da kwanan nan ya sake jaddada biyayyarsa ga Kwankwaso, tare da cewa ya yi wata ganawa da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Maganar takarar Hanga a NDC
A cewar Gwangwazo, ƙin bai wa Hanga wata takara a sabuwar haɗakar siyasar NDC ya nuna cewa Kwankwaso ba ya ganin darajarsa.
Daily Trust ta rahoto ya ce:

Kara karanta wannan
Babban jigon APC a Arewa ya yi magana kan barin jam'iyyar bayan Tinubu ya zabi Shettima
"Mun zo ne domin maraba da dawowarka daga tafiyar jinya, sannan mu jajanta maka kan irin wulakancin da Jagora ya yi maka.
"Duk da dogon lokacin da ka shafe kana tare da Kwankwaso kana mara masa baya, a bayyane yake ya nuna cewa ba ka da wani muhimmanci a wajensu.
"Domin tabbatar da hakan, Kwankwaso ya ƙi ba ka kowace takarar zaɓe a cikin NDC duk da irin sadaukarwar da ka yi. Wannan ya isa ya nuna maka wanene ainihin mai cin amana."

Source: Facebook
Maganar shigar Hanga APC
Jagoran tafiyar ya kuma roƙi Sanatan da ya koma APC tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf, yana mai tabbatar masa cewa za a ba shi muhimmanci da daraja a cikin jam’iyyar.
Ya ce:
"Mun zo ne domin mu roƙe ka da ka dawo ka shiga APC tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda za a daraja ka kuma ka kasance mai muhimmanci.
"Ba ma yi maka alƙawarin tikitin Sanata ba, domin gwamnan ya riga ya daidaita batun 'yan Majalisar Tarayya da na Jiha. Amma muna son ka dawo inda za a ba ka ƙima."

Kara karanta wannan
Lokaci ya fara ƙurewa, Tinubu ya sanya wa'adin da kowane ɗan Najeriya zai mallaki NIN
Sanata Hanga ya soki Obi
A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanata Rufai Hanga da ke tare da Rabiu Musa Kwankaso ya soki jamm'iyyar NDC.
Sanata Hanga ya bayyana cewa babu wata alamar da ke nuna cewa dan takarar ADC a 2027, Peter Obi zai kai labari.
Wannan shi ne sabani na farko da ya fara bayyana bayan rashin samun takarar Sanata Hanga a NDC duk da cewa yana tare da Kwankwaso.
Asali: Legit.ng