‘Yan PDP sun fara lissafin wuri domin lashe zaben Shugaban kasa a 2023

‘Yan PDP sun fara lissafin wuri domin lashe zaben Shugaban kasa a 2023

Wani rahoto da mu ka samu ya bayyana mana cewa jam’iyyar hamayya ta PDP ta fara kokarin ganin yadda za ta dawo mulki a 2023.

Yanzu haka jam’iyyar PDP ta soma tado kirazanta domin lashe zaben shugaban kasa mai zuwa. A 2023 ne wa’adin shugaba Buhari zai cika.

Jagororin PDP da ke fadin kasar su na nan a farke har yanzu, bayan haka kuma jam’iyyar adawar ta na rike da gwamnonin jihohi 15 a yau.

Masu hasashen siyasa su na ganin cewa zaben da za ayi a 2023, zai kasance tsakanin PDP ne kawai da kuma jam’iyyar APC da ke kan mulki.

Bayan ta sha kashi a 2019 a hannun APC da shugaban kasa Muhammadu Buhari, PDP ta ja baya, ta fara shiryawa babban zaben da za ayi a 2023.

KU KARANTA: Gwamnoni 3 za su nemi kujerar Shugaban Gwamnonin PDP

Jam’iyyar PDP ta na ganin za ta iya kai labari a zabe mai zuwa ne saboda ganin cewa ba za ta yi takara da Muhammadu Buhari ba a lokacin.

Sakataren yada labarai na PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, ya tabbatar da cewa PDP ta na kokarin yin wasu gyare-gyare domin 2023.

Sai dai Kola Ologbondiyan ya bayyana cewa kawo yanzu PDP ba ta fara maganar inda za ta kai takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023 ba.

Ologbondiyan ya ce sun fara yunkurin jan hankalin ‘Yan Najeriya tare da kokarin dinke duk wata baraka da ta ke cikin gidanta domin ta yi nasara.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel