Har ila yau: Kotun koli ta kara matsa wa gaba da ranar yanke hukunci a kan kujerar gwamnonin Sokoto, Benuwe da Imo
Kotun koli ta dage sauraron daukaka karar dake kalubalantar zabukan gwamnonin jihohin Bauchi, Benuwe da Filato.
Alkalin alkalan Najeriya, Ibrahim Tanko Muhammad, yayi wannan sanarwar ne a ranar Talata a Abuja. Yace kotun zata sanar da sabuwar ranar cigaban da sauraron daukaka kararrakin.
An dage karar ne don baiwa kotun kolin damar fuskantar shari’un da yakamata a kammala a ranar 17 da 20 ga watan Janairu a 2020.
A yayin zantawa da manema labarai, lauyan dan takarar gwamnan jihar Filato a karkashin jam’iyyar PDP, Mike Ozekhome, yace dage karar ta biyo bayan daga wasu manyan shari’u daga yau Talata zuwa ranar Juma’a.
Yace wadannan daukaka kara dole ne a kammala shari’unsu kamara yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya tanadar a cikin watan nan.
Ozekhome yace, “Daukaka karararrakin da wa’adinsu zai kare a ranar 17 da 20 ga wata ne aka bai wa muhimmanci. Namu da wa’adinta zata cika a ranar 28 ga watan Janairu ne aka dage saboda lokaci ba zai bada dam aba.”
Ya bayyana damuwarsa ta yadda gwamnati ta kasa kar yawan alkalan kotun koli zuwa 21 a maimakon 15 da a halin yanzu suke sauraron daukaka kara. Yace hakan zai rage wa alkalan aiki wanda zai tabbatar da kammala shari’u a kan lokaci.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng