Ishaku, Tambuwal da Ortom za su nemi Shugaban Gwamnonin PDP

Ishaku, Tambuwal da Ortom za su nemi Shugaban Gwamnonin PDP

Mun samu labari cewa an fara shirye-shiryen wanda zai zama sabon shugaban gwamnonin babbar jam’iyyar PDP mai hamayya a Najeriya.

Kamar yadda mu ka samu labari daga This Day, gwamnoni akalla uku ne su ka burin darewa kan kujerar da gwamna Seriake Dickson zai bari.

Jaridar This Day ta bayyana cewa masu neman wannan kujera su ne Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal Darius Ishaku, da Samuel Ortom

Ana ganin cewa wannan kujera ta na da tasiri wajen zaben wanda jam’iyyar PDP za ta ba tikitin takararta na shugaban kasa a zabe mai zuwa.

PDP ta na da gwamnoni 15 a halin yanzu, amma wannan karo za ta fito da shugaban gwamnonin na ta ne daga bangaren Arewacin Najeriya.

KU KARANTA: Tinubu ya cancanci ya gaji Shugaba Buhari ba Ibo ba – Kungiya

Ishaku, Tambuwal da Ortom za su nemi Shugaban Gwamnonin PDP
Ishaku da Ortom su na cikin wadanda ake yi wa harin gwamnan gwamnonin PDP
Asali: UGC

Gwamna Seriake Dickson wanda ke rike da wannan kujera zai sauka ne kwanan nan ganin cewa wa’adin mulkinsa ya cika a jihar Bayelsa.

Dadaddun gwamnonin da jam’iyyar PDP ta ke da su a yankin Arewacin kasar nan su ne na Sokoto, Taraba da Benuwai da mu ka lissafo.

Wasu su na ganin cewa Alhaji Amini Waziri Tambuwal, wanda ya nemi tikirin takarar shugaban kasa a PDP a bara ne zai samu wannan kujera.

Aminu Tambuwal ya taba rike shugaban majalisar wakilai, kuma yanzu haka shi ne mataimakin gwamnan gwamnonin Najeriya gaba daya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel